Hukumar gudanarwar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gashuwa (FUGA) ta amince wajen nada Farfesa Maimuna Waziri a matsayin sabuwar shugabar jami’ar, wadda ita ce ta uku a jerin shugabanin makarantar kuma mace ta farko da za ta jagoranci ragamar jani’ar.
Hukumar gudanarwar ta sanar da hakan da yammacin ranar Asabar, a takardar sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen kula tare da harkokin yada labarai a jami’ar, Mista Usar Ignatius.
Hajiya Maimuna wadda Farfesa ce a fannin ilimin kimiyyar hada magunguna (Chemistry) ta gaji shugaban jami’ar mai barin gado, Farfesa Andrew Haruna wanda zangon mulkinsa zai kammala a farkon watan Fabarairun 2021.
Bugu da kari, Waziri ta samu nasarar shugabancin kujerar jami’ar ne bayan da ta doke farfesoshi 47 wadanda su ka fafata a zaben wanda ya gudana ranar 16 ga watan Junairun 2021.
A karshe, da yake taya sabuwar shugabar murna, shugaban hukumar gudanarwar ya bukace ta da rungumi daukwacin ma’aikatan jami’ar tare da aiki da kowane bangare don ci gaban jami’ar.