Connect with us

LABARAI

Farfesa Moghalu Ya Samu Tikitin Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar YPP

Published

on

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasarnan, Farfesa Kingsley Moghalu, ya zama dan takaran neman shugabancin kasarnan a karkashin tutar Jam’iyyar YPP.
Kingsley Moghalu, ya zama dan takaran ne a wajen babban taron wakilan Jam’iyyar na farko da ya gudana ranar Asabar a Abuja, inda kuma aka gudanar da zaben fid da gwani na wanda zai tsaya wa Jam’iyyar takarar shugabancin kasar nan.
Kingsley Moghalu, ya sami kuri’u 243 daga cikin kuri’un wakilai 253 da aka tantance, wanda hakan ya ba shi daman doke abokin hamayyar sa, Donald Igwegbu, hakan ne kuma ya sanya shi janye masa.
Mista Igwegbu, ya bayyana shawarar sa ta janyewa ne da cewa, ba ya janye ne domin bai cancanta ya tsaya takarar shugabancin kasar a zaben na 2019 ba, sai domin Kingsley Moghalu, yana da manufa iri daya da na shi.
Da yake jawabin amsan sakamakon zaben, Kingsley Moghalu, cewa ya yi, Nijeriya tana da bukatar shugaba ne wanda duk duniya sun san cancantar sa, ba ‘yan siyasan da suka kasa ciyar da kasannan gaba ba.
“Har kimanin shekaru 40, ana ganin kasar Sin a matsayin kwandon shara, ta tara al’ummun da suka yi mata yawa, ba ta iya tsinana ma kanta komai, tattalin arzikin ta ya ruguje a bisa tsare-tsaren shekarun da suka gabata kafin nan.
“Amma a yau, za su iya nu na yatsa su dauki hoto da shi, kusan dukkanin shugabannin Afrika a kullum suna kan hanyar zuwa kasan ta Sin da kokon baran su a hannu, suna neman ta taimaka ma su. Wannan shi ne sakamakon da duk kasar da take da shugabanni masu tsinkaya za ta samu.
“Amsan wannan tikitin tsayawa takaran da na yi daga wannan hamshakiyar Jam’iyyar, ina mai shaida maku cewa, tabbas Nijeriya za ta bunkasa a gida da waje a zamanin mu.
Kingsley Moghalu, ya ce ya shiga Jam’iyyar ta YPP ne domin yana da tabbacin za ta gaji sunan na ta na, Ci gaba.
Ya ce lokaci ya yi da Nijeriya za ta fita daga yayin barnatarwa, cin hanci da rashawa, da kuma zaban shugabannin da ba su cancanta ba, wadanda su ke mayar da Nijeriya baya.
“Yanzun lokaci ne na yin zabi a tsakanin ci gaba da zama tare da nu na bambancin kabila da na Addini, a bangare guda kuma zabi ne na a hada hannu domin a gina hamshakiyar kasa.
“Zabi ne a tsakanin ‘Yanci da kuma ci gaba da zama a cikin bauta, a karkashin gurbatattun ‘yan siyasa, da kuma tsakanin talauci da wadata ga talakawan kasar mu, da tsakanin rashin aikin yi, da tsakanin rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa ta mu Nijeriya.
Kingsley Moghalu, ya kuma nu na damuwar sa kan yadda Shugaba Buhari ya ki sanya hannu a kan dokar zabe wacce aka yi wa gyaran fuska.
Tun da farko, Shugaban Jam’iyyar, Bishop Amakiri, cewa ya yi, Nijeriya ba tana cikin kunci ne saboda ta rasa albarkatun kasa da al’umman da za su alkinta su ba.
“A matayinmu na Jam’iyya za mu mayar da hankali wajen cin gajiyar yawan da muke da shi a kasar nan.
“Wajen sanin tattalin arzikinmu, Ilimi ne zai kasance ginshikin ci gabanmu, domin ba wata kasar da za ta bunkasa ba tare da ilimin ba,” in ji shi.
Kan batun sake fasalin kasa kuwa, cewa ya yi, matsayin Jam’iyyar ta YPP a sarari yake, fasalin yadda kasarnan ke a kai yanzun ba mai dorewa ne ba.
“Babban jigon hanyar da za mu tafiyar da tattalin arzikinmu kamar na sauran sassan duniya shi ne mu sake fasalin tattalin arzikin na mu, tsarin siyasar mu ta yadda za a baiwa kowane sashe cin gashin kanshi.
“Jam’iyyarmu za ta dauki kwakkwaran matakin ganin an yi da kowa wajen ganin yanda za a raba wa kowa hakkin sa.
Ya kuma ce, Jam’iyyar a shirye take da ta karbi ragamar shugabancin kasarnan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: