Daga CRI Hausa
Wani kwararren kasar Habasha ya bayyana cewa, manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a shirinta na yaki da talauci muhimmin darasi ne ga kasashen Afrika a kokarin da kasar ta yi wajen raya tattalin arzikinta da kuma tsame miliyoyin mutanenta daga kangin talauci.
A hirarsa da kamfaninn dillancin labarai na Xinhua, Costantinos Bt. Costantinos, farfesa a sashen nazarin dabarun shugabanci a jami’ar Addis Ababa ta kasar Habasha, ya ce, salon da kasar Sin ta yi amfani da shi ba kawai ya tsame mutane daga talauci ba ne, har ma ya taimaka wajen bunkasa karfin tattalin arzikin GDPn kasar, da cigabanta karkashin shirin na yaki da fatara.
Kwararren, wanda ya taba yin aiki a matsayin mashawarci a fannin raya tattalin arzikin kungiyar tarayyar Afrika, da hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD, ya kara da cewa, dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika zai iya kasancewa a matsayin wani muhimmin dandalin da zai baiwa Sin da Afrika damar yin musayar kwarewa wajen yaki da fatara.
Game da yaki da fatarar, kwararren ya bayyana cewa kasar Sin tana da cikakkiyar kwarewa, kuma a shirye take ta yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, wajen cimma wannan buri, inda ya jinjina manyan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen tsame miliyoyin mutanenta daga talauci. (Ahmad)