Bello Hamza" />

Fargaba: ‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Kai Hari Sakkwato

Wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi barazanar kai wata mummuman hari a wasu kauyukan jihar Sakkwato 4 da wasu kauyukan dake a makwabciyar jihar Zamfara, kamar dai yadda kafar watsa labarai ta DAILY NIGERIAN ta ruwaito.
Wasu ‘yan kauyen da suka tattauna da ‘yan jarida a ranar Asabar sun ce ‘yan ta’adda sun rubuto wasika ne zuwa ga kauyuka 4, kamar haka Ruwan Tsamiya da Kursa da Gandi dukkansu dake a yankin karamar hukumar Rabah ta jihar Sakkwato.
Majiyar ta kuma ci gaba da bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun aika wasikar gargadi zuwa kauyukan Kaiwar Dawa da Malela duk a cikin karamar hukumar Rabah.
“’Yan ta’adda sun bukaci makudan kudade ne daga hanun wani hansjakin mai kudi mai suna Alhaji Mani Shehu, wani manomin shinkafa, kamar dai yadda ani mai suna Mallam Zaidi, ya bayyana wa kafar DAILY NIGERIAN.
“A halin yanzu ‘yan kauyen na tatara kudade don biyanb fabsar saboda su kauce ma harin da ake shirin kai musu, soboda in har sun ki basu san abin da zai iya faruwa ba,”
Wani malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo Unibersity, Sakkwato, Mansur Buhari, ya bayyana wa DAILY NIGERIAN cewa, wasu kauyan sun kira shit a waya suna yi masa korafin halinda ‘ynta’addan ska sanya su da kuma bukatar ta su.
Jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sanda na Sokoto, Cordelia Nwawe, ya karyata kofarin da ‘yan kauyen suke yi, yana mai cewa, har yanzu rundunar ‘yan sanda basu karbi wani rahoto daga wajen jama’ar kauyen ba.
Misis Nwawe ta kuma lura da cewa, a halin yanzu yankin na karkashin wani kariya na musamman daga jam’an ‘yan sanda.

Exit mobile version