Fargabar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 13 Ta Karu
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fargabar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 13 Ta Karu

byYusuf Shuaibu
2 years ago
Ruwa

Akwai yiyuwar wasu jihohi a Nijeriya za su fuskanci ambaliyar ruwa nan da kwanaki masu zuwa, yayin da kasar Kamaru ke shirin bude tekun Lagdo da ke gabar kogin Benuwai.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa (NEMA), jihohin sun hada da Adamawa, Taraba, Benuwai, Nasarawa, Kogi, Filato, Gombe da Bauchi da dai sauransu.

  • Rage Radadin Cire Tallafi: Gwamnati Ta Baiwa  Kowacce Jiha Naira Biliyan Biyu A Kashin Farko
  • Xi Ya Taya Wata Jami’a Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwa, Sannan Zai Ba Da Jawabi A Yayin Bikin Bude CIFTIS Na 2023

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje ta fitar mai dauke da kwanan watan Agusta 25, 2023, ta sanar da hukumar NEMA kan wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Kamaru ya fitar a hukumance cewa jami’an sun yanke shawarar bude mashigar madatsar ruwa tekun Lagdo a cikin kwanaki masu zuwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a magudanar ruwan da ke yankin Arewacin Kamaru.

“Yana da kyau a sani cewa lokacin fitar da ruwa ya zama dole, hukumomin madatsar ruwa na Lagdo za su fitar da ruwa kadan ne kawai a lokaci guda don ragewa da kuma guje wa barnar da ruwan da aka saki zai iya haifarwa a bakin kogin Benuwai a Kamaru da Nijeriya

“Saboda haka, za a yaba idan hukuma ta dauki dukkan matakan da suka dace da kuma ayyukan da za su rage barnar tare da wayar da kan jama’ar da ke zaune a irin wadannan wuraren don yin taka tsantsan,” in ji ma’aikatar.

Gwamnatin tarayya ta ce mutane 3,219,780 ne ambaliyar ruwan ta shafa a shekarar da ta gabata, wanda ya zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, mutane 1,427,370 suka rasa matsugunansu, 2,776 suka jikkata, yayin da 612 suka mutu.

Masu ruwa da tsaki a ko da yaushe suna danganta barazanar ambaliya daga madatsar ruwa ta Lagdo da gazawar hukumomin Nijeriya wajen kin gina madatsar ruwan Dasin Hausa, wanda ke daura da kogin Benuwai, kamar yadda aka yi yarjejeniya a 1982.

A shekarar da ta gabata ne dai tsohon ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu, ya yi zargin cewa Kamaru ba ta sanar da Nijeriya ba game da sakin ruwan tekun Lagdo.

“Ana sakin ruwa a wannan dam a kowani lokaci, kuma idan aka saki ruwan ba tare da sanarwa ba, yana shafar al’ummomin da ke kasar nan.

“Mun yi kokari sosai mu da su don sanya hannu kan wata yarjejeniya na sanar da Nijeriya game da sakin ruwan tekun.

“An sanya hannun a shekarar 2016. Tun daga lokacin, duk shekara idan damina ta kama, duk shekara hukumar kula da ruwan ruwa ta Nijeriya ce ke kiran su don sanin yawan ruwansu.

“Ba za mu iya dora laifin ambaliya a wannan shekarar a kan Kamaru ba. Za mu dora musu laifin karya ka’idojin yarjejeniya ne kawai,” Adamu ya fada a lokacin da yake kare kasafin kudi a majalisar dattawa.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a tsawon shekarun da suka gabata, an samu ambaliyar ruwa mai yawa a jihohin kasar nan da dama da ake dangantawa da sakin ruwa daga tekun Lagdo.

Haka kuma an samu barnar ambaliya a shekarar 2022 wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi na biliyoyin naira.

Mai magana da yawun hukumar NEMA, Manzo Ezekiel, ya bayyana cewa sako ruwan tekun Lagdo zai shafi jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai, Nasarawa da Kogi da dai sauran su.

“Daga Kogi zuwa Jihar Delta idan aka samu karuwar ruwa a Jihar Neja zai zama babban kalubale. Wadannan jihohi ne da ke kan kogin kai tsaye, akwai wasu jihohin da abin ya zai shafa saboda an rufe kogin kuma ba su da wurin da ruwa zai ci gaba da kwarara, irin wadannan wuraren ma za a iya ambaliya kamar wasu sassan Gombe, Filato, Bauchi.

“Jihohin farko su ne wadanda ke kan hanyoyin kogin, amma sauran na iya shafa ne sakamakon tasirin ruwan.”

Ya ce fitar da ruwa da ya wuce gona da iri daga tekun Lagdo bai zo wa NEMA da mamaki ba kamar yadda hukumar ta yi a shirinta na ambaliyar ruwa na wannan shekara.

Ya ce hukumar NEMA ta sanar da gwamnonin jihohi yiwuwar afkuwar ambaliya, kuma galibinsu sun dauki matakai da suka dace ta hanyar share magudanan ruwa da suka toshe da sauran hanyoyin da ke haifar da ambaliya.

Ya ce hukumar ta kuma shawarci gwamnonin da su ware kudade na musamman domin bala’o’i da suka hada da ambaliyar ruwa.

Ezekiel ya ce a baya hukumar NEMA ta sha gaya wa jihohin da su kwashe mutanen da ke bakin ruwa zuwa wuraren da ba za su kai ga ambaliyar ruwa a bana ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
Kallo Ya Koma Sama: Greenwood Ya Koma Getafe

Kallo Ya Koma Sama: Greenwood Ya Koma Getafe

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version