Daga El-Mansur Abubakar, Gombe
A ranar Juma’ar da ta gabata ne da misalin ƙarfe goma na dare wasu Matasa da ake kyautata zaton ‘yan barandar siyasa ne a Gombe suka far wa shugaban Matasa na Jam’iyyar APC na Unguwar Herwagana a fadar jihar Shafi’u Idris, a kwarin unguwar Misau a lokacin da yake ƙoƙarin tafiya gida suka masa dukan kawo wuƙa suka yi awon gaba da Babur ɗinsa ƙirar Jinchen Kasea.
Da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP A Yau a kwance a gadon asibiti a dakin kula da marasa lafiya na gaggawa na Accident and Emergency na asibitin ƙwararru dake fadar jihar Shafi’u Idris, ya ce, wannan hari da aka kai masa na neman kashe shi ya biyo bayan wata hira da ya yi ne a gidan Rediyon Progress FM kan gwamnatin Gombe.
Ya ce, a lokacin da ya shiga wannan kwari da niyyar zai ƙetare zuwa gidansa a hayin kwarin Misau kawai sai yaga wasu Matasa sun sha gaban sa nan take ɗaya ya jifga mar sanda a geya daya kuma ya soka mar wani
“A lokacin da na shaƙi wannan hodar sai hankali na ya gushe kuma ga zafin duka sai naga idan na faɗi a kwarin nan bani da wanda zai taimaka min kuma za su iya kashe ni da ƙyar nayi ta maza na daure na
fita a kwarin jiri yana diba ta sai na faɗi kusa da wasu mutane waɗanda sune suka taimaka min suka kai ne asibiti kusan ƙarfe goma sha ɗaya na dare” inji Idris.
Shugaban Matasan APC na Herwagana ya ce, tunda mutanen nan suka ɗauke shi suka kai shi asibiti bai san inda hankalinsa yake ba sanda ya kwana biyu sannan ya farfaɗo ya gane inda yake ya iya fara magana da mutane shi ne har yake zantawa dani kan abunda ya faru da shi.
Shafi’u Idris, ya yi amfani da wannan dama ya yi kira ga shugabanin jam’iyyar su ta APC da cewa yana da kyau su tashi tsaye wajen ganin sun ɗauki matakin kare ‘Ya’yansu daga irin wannan hari domin idan aka bari haka zai ci yau an masa gobe wani za’a yi wa.
Ya kuma ce, bayan hirar farko da ya yi akan gwamnatin jihar Gombe ya sake yin wata hira kan halin da Malaman Makaranta suke ciki a jihar shi ne abunda yake zargi kenan sannan sai ya ce, a lokacin da matasan suka tare shi yaji ɗaya daga cikin su yana faɗin cewa tunda yana shiga Rediyo yana zargin gwamnati sai sun kashe shi shi yasa yake zargin gwamnatin na da hannu kan wanna hari da aka masa.
Ya godewa wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar su ta APC da suka ziyarce shi a asibiti suka jajanta masa na wannan iftila’in da ya faru dashi wasu kuma suka masa waya inda ya ce, yaji dadin hakan na kula da suka masa.
LEADERSHIP A Yau, tayi ƙoƙari dan jin ta bakin jami’an Yan sanda ko sun sami labarin wannan al’amari da ya faru amma lamarin ta ci tura.