Connect with us

LABARAI

Fasahar Kasuwanci: ‘ELAB PROVIDER SOLUTION’ Ta Yi Taro Da ‘Yan Kasuwar Sabon Garin Kano

Published

on

Kamfanin “Elab solution Provider”ya gudanar da wani taro na musamman kan sanin makama ga ‘yan kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi, wacce aka fi sani da Kasuwar Sabon gari kan yadda za su rika  biyan haraji da kuma hanyoyin bunkasa ci gaban kasuwancinsu ta hanyoyin fasahar zamani.

 

Taron wanda ya gudana a Kano bisa jagorancin Sarkin kasuwar Sabon Gari, Alhaji Nafi’u Nuhu Indabo ya sami halatar wasu daga shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwar da mambpbinsu.

 

A cikin bayaninsa, Darakta na ‘Elab solution provider,’ Alhaji Aminu Ibrahim Danmasani ya ce taro ne na sanar da ‘yan kasuwar da ilimantar da su hanyoyi da za su yi mu’amala da su domin tafiya daidai da zamani a dukkan harkarsu ta biyan haraji ga Hukumomi da kuma yadda za su rika amfani da manhajoji na fasahar zamani wajen harkar su ta saye da sayarwa ta hanyar manhajar da suka samar na kasuwannin Kano.

 

Alhaji Aminu Danmasani ya yi nuni da cewa tsarin abu ne mai muhimmanci da zai taimaka wajen habakar kasuwanci, kuma zai samar da hanya ta budaddiyar kasuwa a kowane lokaci a kowane yanayi ga ci gaban ‘yan kasuwar.

 

Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Kasuwar Sabon Gari, Alhaji Nafi’u Nuhu Indabo ya nuna matukar farin cikinsa da wadannan tsare-tsare ta “Elab Provider solution,” wanda ya ce idan ‘yan kasuwar Kano suka yi amfani da su za su taimaka sosai wajen buda harkokin kasuwanci.

 

Alhaji Nafi’u ya ce ‘yan kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi za su baiwa tsarin na ‘Elab ‘goyon baya don ya kai ga nasara, wanda in haka ta samu, su ne iyan kasuwa da za su fi amfana.

 

A yayin taron, Injiniya Ja’afar Muhammad, wanda shi ne  Jami’in tsare-tsare na “Elab  Provider Solution” ya yi bayanai masu gamsarwa kan shirin, inda ya ce sabon tsarin zai kunshi bayanai muhimmai na gida da inda ake kasuwanci da kasuwa da layin da shagon dan kasuwa yake da irin kayan da yake da su da sauran muhimman bayanai da za su taimaka wajen habaka harkokinsu.
Advertisement

labarai