Fasahar Sin Ta Yaki Da COVID-19 Ita Ce Mayar Da Rayuka Matakin Farko

Ya zuwa ranar 18 ga wata, adadin mutanen da cutar numfashi ta COVID-19 ta shafa a birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin ya ragu zuwa 109, kana yawan wadanda cutar ta yi tsanani a jikinsu shi ma ya ragu zuwa 22, akwai wahala matuka ga likitoci yayin da suke kokarin ceton rayuka.

Alkaluman kidididgar da hukumar lafiya ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar fiye da 2500 wadanda shekarun haihuwarsu suka kai sama da shekaru 80 a birnin Wuhan, an yi nasarar ceton rayukansu da kaso 70 bisa dari, a cikinsu, tsoffi guda bakwai wadanda shekarun haihuwarsu suka kai 100 sun riga sun koma gida bayan sun warke, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin tana aiwatar da ka’idar mayar da rayuka a gaban kome yayin da take yaki da cutar.
Yayin da kasar Sin take kokarin dakile annobar, har kullum tana maida hankali kan aikin ceton rayuka, inda aka nuna “saurin kasar Sin” domin ceton rayuka cikin hanzari.
Domin cimma burin shawo kan annobar a birnin Wuhan da sauran sassan lardin Hubei, gwamnatin kasar Sin ta tura likitoci sama da dubu 42 cikin gaggawa zuwa wuraren, kana an gina asibitoci da dama domin ba da jinya ga wadanda suke bukata a kan lokaci, a sa’i daya kuma, an yi jigilar kayayyakin kiwon lafiya da na’urorin likitanci kamar na’urar numfashi ta ECMO zuwa birnin Wuhan daya bayan daya.
Har kullum gwamnatin kasar Sin tana mayar da rayukan al’ummunta a matakin farko, musamman ma rayukan tsoffi da wadanda suke fama da cututtuka da kuma matalauta.
Ya zuwa ranar 6 ga wata, matsakaicin kudin jinya na kowanen mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar COVID-19 ya kai kudin Sin yuan dubu 21.5, kana matsakaicin kudin jinya na kowanen mutum wanda cutar ta yi tsanani a jikinsa ya kai kudin Sin yuan dubu 150, wasu kalilai wadanda cutar ta yi tsananin matuka a jikinsu kuwa sun kashe kudin Sin yuan sama da dubu 100 ko miliyan daya a kowanensu, gwamnatin kasar Sin ce ta biya kudin bisa inshorar kiwon lafiya, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun warware matsalolin da al’ummun kasar suke fuskantar yayin da suke samun jinya a asibiti.
Hakika yayin da ake fama da rikici, yadda ake ceton rayukan al’ummu jarrabawa ce ga manufar kasa da karfin gudanar da harkokin kasa, kowa yana da rai guda daya kawai, a don haka, dole ne a nuna biyayya da kuma kiyaye rayuka, bai kamata ba a nuna son kai, ya dace a kara karfafa hadin kai, domin ceton karin rayuka, kana bai dace ba ‘yan siyasa su dora laifi kan wasu da suke fakewar “Kila wannan shi ne rayuwa”.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version