Fashewar tankar mai a yankin Jebba dake karamar hukumar Moro a jihar Kwara tayi sanadiyyar rasa rayuka akalla 6 da kone gine-gine 30.
An rahoto cewa dai, motar ta kwace ne a hannun direbanta inda ta fada cikin wasu gine-gine nan take kuma ta fashe sakamkon man da ke tsiyaya.
“Fashewar motar ta hallaka mutum 6, gidaje 30 sun kone tare da shaguna.” Inji wani Wanda yake nan lamarin ya afku.
Sannan Daga bisani jami’an kashe gobara na jihar suka iso wurin suka kashe wutar, bayan ta cinye wadancan gidajen da shaguna.
Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ta hannun Sakataren Yada Labaransa, ya jajanta wa iyalai da wanda ibtila’in ya shafa.