Fashin Bakin Malamai Kan Rashin Alfanun Yawaitar Masallatan Juma’a A Nijeriya  

Masallatan

 

 

 

Daga Khalid Idris Doya

A halin yanzun Malaman Addinin Musulumci sun maida gina Masallatan Juma’a a matsayin gasa a tsakaninsu wanda hakan ya janyo yawaitar Masallatan Juma’a a lunguna da sakuna wanda hakan ke rage armashi da taruwar Musulmai a duk ranar Juma’a don gabatar da Sallar Jumma’a ko sauraron huduba na bai-daya a cikin gari ko yanki.

A shekarun baya gari kan amsa sunansa da ganin cinciridon mutane a duk ranar da Juma’a ta zago wanda hakan ke zama abun sha’awa da kara yalwata son juna, hadin kai da fahimtar juna a tsakani. Sai dai a ‘yan shekarun nan lamuran sun na baya inda ake samun rukunin masallatan Juma’a kashi-kashi a cikin unguwanni, yanki ko gari.

Bincike ya nuna cewa lokutan sallar Juma’a a fadin kasar nan ba zai kirguwa ba, inda wasu ke farawa tun 12 da wasu mintina na rana wasu kuma har zuwa biyu ma da rabi. Sannan, a da baya al’umma kan maida hankali ga Khudumar Juma’a da babban Limamin gari ke yi don samun bayanin halin da ake ciki ko tunarwa daga gareshi, amma yanzu huduboni daban-daban jama’a ke ji ranar Juma’a.

Shi hakan cigaba ne ko akasinsa. A bisa wannan lamarin, mun hada rahoton musamman a wannan makon inda muka yi zanta da malaman da abun ya shafa daga bangarorin Ahlul Sunnah, Darika da na Shi’a domin jin yadda kowani bangaren ya ke kallon wannan lamarin na yawaita gina masallatan Juma’a.

Dakta Ibrahim Adamu Umar Disina, babban Limamin Massalacin Juma’a na ‘Masjidul Rahma da ke kan titin Wunti a cikin garin Bauchi’ kuma Darakta-Janar na gidan talabijin din Sunnah TB, ya bayyana wa LEADERSHIP Hausa cewa wasu masallatan Juma’an ana bude su ne da wata manufa ba don Allah, yana mai cewa akwai bukatar a cike wasu sharuddan kafin bude masallacin Juma’a a cikin al’umma.

A cewarsa: “Yaiwatar masallatai a gaskiya za a kasa wannan batun gida biyu. Akwai wasu masu kyau akwai kuma wasu marasa kyau. Bangaren masu kyau za ka iya cewa idan jama’a suka yawaita in guri ya yi kunci babu laifi a kara samun yawaitar masallatai daya-biyu-uku gwargwadon bukata, ko kuma a ce guri ya yi nisa wanda zuwa wajen massallaci zai wahalar da wadanda suke nesa idan an samu halin da wani wajen da zai kai na massalacin Jumma’a nan ma in sun yi Massallacin Juma’a ba ka iya cewa sun yi laifi ba.

“Amma kuma akwai wasu manufofi wadanda su kuma marasa kyau ne wadanda muke gani daga cikin abubuwan da suke sanya bude massallatan Juma’a wani lokacin akwai bukata ta kashin kai daga su bangaren wadanda suke son su jagoranci massallatan (Malamai kenan), ka ga wani yana son a sanshi ne shi ma ya samu tasa tawagar ko gurin da zai rika zama jagora ko shugaba, wannan ya sa da yawa daga cikin wasu masallatan da ake budewa ba a da bukatarsu.

“Na’am za ka ga masallaci kusa da kusa a unguwa daya ba ma su cika, to ka ga wannan ka sani manufa ce marar kyau. Wani lokacin kuma akwai manufa ta siyasa, nan ma manufa ce marar kyau, wani lokacin tsakanin kungiyoyin addini wadanda Musulunci bai hana wani sashin ya bi wani sashi jam’i ba; domin duk mutumin da in ya yi sallah shi kadai Allah zai karba haka nan kuma idan ya jagoranci mutane sallah Allah zai karbi sallar sa da na mamunsa. Saboda haka sabanin fahimta kadan bai kai a ce har an raba massallatai ba. To amma wani lokacin sai ka ga irin wadannan an samu masallatai barkatai saboda banbance-banbancen akida wanda yake kuma wani lokacin ba manufar Allah ba ce ba, don haka da zarar mutum ya bude masallaci don wata manufa ba don Allah ba hakan bai da kyau.”

“Na biyu wani lokacin za ka samu wato ba ma malaman bane wasu ne daga cikin jagororin masallatan ko mawadata ko ‘yan siyasa suke budewa wadanda suke tare da su masallatai don dai su ce sun musu wani abu, kamar yadda duk wanda ya goya wa dan siyasa baya zai so a ce shi ma yana son ka masa wani abu ko ya zama ka kyautata masa ta wani fannin da yake so. Hakan ya sanya ka ga ana ta bude wa malamai masallatan Jumma’a kamar yadda muke ganin sau da yawa idan malamai sun goyi bayan ‘yan siyasa har su kai ga samun nasara a madafun iko za ka ga abun da za su saka musu da shi shi ne su bude musu masallatan Jumma’a ba tare da lura da bukatar hakan ko ba wannan bukatar ba.”

Ya kara da cewa, “Za ka ga kuma wani lokacin ‘yan siyasa na amfani da hakan don cimma manufofinsu na siyasa ka ga duk wadannan abubuwan sam ba su da kyau. A takaice yawaitar masallatan Juma’a alamu ne daga cikin alamun tashin alkiyama, na’am daman Annabi (S) ya fada cewa yana daga cikin alamun tashin alkiyama mutane za su yi ta gasar kawata masallatai, kawatashi ba da karantarwa ba ko nusar da mutane abin da ke kan daidai ba, a a kawata shi ko da yawaita ko kuma da kwalliyar ginin ko dai da wani abin da Malami zai so a ce nasa ya fi na Malam wane ko ma ya fi na kowa. Massalaci an maida shi daga wurin yi wa Allah ibada zuwa wurin gasa ka ga wannan manufa ce da bata da kyau.”

Disina ya kara da cewa malaman Musulunci sun nassanto cewa babban abin da ake bukata a masallacin Juma’a shi ne haduwar mutanen gari dukkan Juma’a, ba za a kara bude (sabo) wani masallacin ba sai in akwai matukar bukatar hakan.

“Wanda a halin da muke ciki a Bauchi din nan kawai akwai sama da masallatan Juma’a 150 (a cikin kwaryar garin) babu bukatar hakan a gari irin wannan, wannan ya sanya za ka ga da yawa daga cikin massallatan kamar masallaci ne da ya dace ake salloli biyar (Asuba, Azahar, La’asar, Magriba da Ishah) saboda rashin dacewar budewar balle a maida su na Juma’a”.

Daga bisani Dakta Disina ya jawo hankalin malamai, kungiyoyin addini, ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da suke daukan bude masallatai a matsayin gwaninta da cewa kowa ya ji tsoron Allah da gane cewa muddin aka ki yin addini don Allah aka yi don wata manufa la shakka sunan wannan aikin na banza babu lada a ciki sam.

“Sannan ina kuma kira ga hukumomi tun da akwai ma’aikatun da suke kula da lamuran addini ya zama suke sanya ido suna shiga cikin lamuran da za su kyautata addinan mutane abu ne a fili irin wannan yawaitar masallatayyan Jumma’a ba mu da bukatarsu saboda haka ya dace gwamnati ta shigo ta sanya hannu a sake tsaftace lamarin ta hanyar samar da wasu dokoki da ka’idojin da mutum ya kamata ya bi kafin ya kai ga bude masallatayyan, wadanda kuma aka gano ba a da bukatarsu kamata ya yi a rufesu,” Inji Dakta Ibrahim Adam Disina

Tahir Umar Sulaiman Gurfa, wani malamin mazhabar Shi’a ne, ya bayyana cewar yawaitar masallatan rabuwar kawuka suke janyowa ba hadin kai ba, don haka ne ya nuna hakan a matsayin ko koma ba.

“Da farko ina cewa batun yawaita bude massallatai lallai ba shi ne yake da muhimmanci ba. Sakamakon yawaita bude masallatai din ya kan jawo matsaloli daban-daban. Da farko a hankalce idan ka duba za ka ga da gaske idan aka samu massallatai masu yawa za ka taras cewa kowanne a cikinsu ba lallai ya zama an cika ba.

“Ka kaddara inda a ce mutanen unguwa za su hadu a massalaci daya su cika domin yin sallar Juma’a abun zai ke bada sha’awa, amma idan a unguwa a misali an samu masallatai har uku to yanzu za ka raba wadannan al’umma kashi uku da ya dace su cika massalaci daya, za ka ga a duk cikin massalaci ukun babu wanda ya cika.”

“A bangaren na biyu wasu kuma sukan bude ne sai kuma su yi abun da Allah da ya ce a bude Massallatan ba ya so. Mene ne Allah ba ya so? Shi ne rarrabuwar kai, Allah yana hani a cikin Al-Kur’ani yana cewa ‘Waa’atasimu Bi Hablil Lahiy Jami’an Walaatafarrakoo’, ‘Ku yi riko da igiyar Allah kada ku rarraba’. To, amma yanzu sai aka maida masallaci wajen rarraba kawuka, mutum zai je masallacinsa ya yi ta antayo suka zuwa ga wasu daban, su ma sai su yi kokari su haifar da nasu massallacin don suke antayo nasu suka ko martanin a kan abubuwan da wancan ke fada a kansu, a maimakon ya zama masallaci ya zama dakin Allah wurin da za a daga kalmar Allah sai ya zama kuma ya zama wajen maida martani.

“Wannan abun da ke faruwa ne a zahirance a cikin al’ummarmu. Yau wani zai hau minbari a cikin massalacinsa ya kafirta wasu gobe su ma su shiga nasu su ce su Musulmai ne (misali), ko kuma nan take a bidi’antar da ku, ku kuma ku zo kuna kokarin cewa ku ba ‘yan bidi’a ba ne.”

“Don haka tabbas haifar da wayaitar massalatai ba cigaba bane ga Addinin Musulumci raunata Musulunci ne ma. Da karfafa Musulunci ne da mun ga Hadisi ko Aya da Allah ya yi umarni cewa a yawaita budewa din, babu Aya ko Hadisi da Allah ya ce a yawaita yin massalatai. Abun da ake so shi ne hadin kai, sannan da kuma alheri ne yawaita masallatan da a zamanin Annabi mun gani, idan ka karanta Al-Kur’ani za ka ga akwai massalacin da aka bude zamanin Annabi wanda Allah ya yi umarni wa Annabi cewa kada ya je wannan Massalacin saboda an bude masallacin ne don raba kan al’ummar Musulmi. To bisa wannan ne nake cewa ire-iren wancan Massallacin wanda aka hana Manzon Allah ya je to akwai ire-iren su fa da yawa sune ma suka fi yawa a wannan zamanin, to gaya min ta yaya za a yi irin masallacin da aka hana Annabi ya je ya bude kuma irinsu ne mafi yawa ya za yi su zama alkairi? Sai suka zama a maimakon su zamo wurin hadin kan Musulmi sai suka koma rarraba kan Musulmi. Mutum ne zai shiga massalaci a rika antayo suka ko zagi ko cin mutunci daga cikin masallacin kuma fa,  ka ga wannan bai kiyaye hurumin massalaci ba.”

Shi ma dai ya nemi gwamnati da hukumomin da abun ya shafa da su ke lura da illar da hakan ke kawowa tare da rage yawaitar masallatan domin hadin kai a tsakanin al’umma, “Bisa la’akari da wannan ne muka cewa lallai akwai hanyar da za a bi a takaita wannan yawan gina wadannan masallatan to abu ne mai kyau sakamakon ba wani abu mai kyau ko kuma ko Kuma wata natija mai kyau da yawan samar da Massalatai ke haifarwa.”

A bangaren Darika kuwa, Allaramma Hamza Muhammad da ke koyarwa a jihar Kaduna, ya bayyana cewar, “Babban matsalar wasu malamai sun sanya son duniya ne fiye da komai. Na ga wani na’ibin da ya bude masallacin Juma’a mai nisan taku bai wuce hamsin na da na limaminsu sakamakon sun Sami sabani wajen rabon kayan azuminda Wani tallafi da aka kawo masallacin.

“Yanzu ta yaya irin wannan za su fadakar yadda ya dace alhali don duniya ya sa suka bude. Gaskiya ina goyon bayan gwamnati ta daina barin kowa kawai na bude masallacin Juma’a yadda yake so domin hakan ma kara rage raba wa jama’a hankali da kuma dosar inda ya dace a sanya gaba ne.”

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Wani Babban Malamin Darika ne a Nijeriya ya taba shaida wa LEADERSHIP Hausa cewa hikimar da ke cikin taruwa domin yin sallar Juma’a shine don hadin kan Musulmai da saduwa da juna,

“Hikimar da ke cikin hakan shi ne, musulunci a kowani lokaci yana son hada kan jama’a ne, hakan ya sanya Allah ya shirya mana yanda Musulmi zai ke haduwa da dan uwansa a kowani lokaci, sai ya zama an mana massallatai domin muke gudanar da sallolin kamsis salawat a ciki, nan kuma aka ce mana a samar da babban massallaci sai ya zama duk Juma’a musulmi na haduwa ana musu huduba da bayyana halin da duniya ke ciki, bayan wannan duk musulunci bai barmu haka ba, sai ya sake bamu damar yanda za’a sake samun hadin kai, sai ya bamu karshen azumi a zo a a hadu a gudanar da babban sallah wanda zai hada mutanen kauye da na birni duk domin a san juna, haka ma na babban sallah duk domin musulmi su hada kansu, ka ga a nan mutanen gari sun hadu.”

 

Exit mobile version