Connect with us

MANYAN LABARAI

Fasto Da Mai Dakinshi Sun Rasa Ransu A Ambaliyar Jihar Imo

Published

on

Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta tabbatar da rasuwar wani Fasto da maidakinsa a wata ambaliyar da aka yi jiya Litinin a garin Owerri na jihar Imo, shugaban hukumar na jihar Imo Mista Evans Ogoh ne ya tabbatar da afkuwar lamarin yau a garin Owerri.

Rahotanni sun shaida yadda ambaliyar ta shafe gidaje da gonaki, masu dimbin yawa a garin Oguta da ke karamar hukumar Oguta ta jihar Imo, hukumar bata bayyana sunan mamatan ba, wasu daga cikin ma’aikatan hukumar da suka bukaci a sakaye sunansu, sun ce laifin hukumar NEMA ne da ta yi biris da gargadin samun ambaliyar da aka yi mata a kwanakin baya.

Hukumar ta ce za ta kara sanya idanu kan yanayin tashin ruwan teku, saboda tashin tekun yana kawo barazanar karuwar ambaliya sosai, kuma hukumar ta ce ta ankarar da mutane tun kafin ambaliyar, a yayin da ta lura da yanayin karuwar tashin ruwan teku.

A karshe hukumar ta bukaci al’ummar da suke zama a yankunan da suke kusa da teku da su, zauna cikin shirin karin samun wata ambaliyar ruwa a nan gaba, sannan hukumar ta umarci wasu kauyuka bakwai wadanda suke fuskantar barazanar ambaliya cikin ‘yan kwanaki, sannan su ma su taimaka wa hukumar wajen sanya ido kan yanayin tashin ruwan tekun.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: