Ba za a ce babu wani abin alheri da al’umar Duniya ciki har da Nijeriya suka girba cikin Shekarar da aka yi ban-kwana da ita ba, wato Shekarar dubu biyu da ashirin (2020). Sai dai, hatta a matakin Duniya bakidaya, an hadu da Babbar annobar da aka yi Shekaru masu yawan gaske da suka gabata, ba a gani ba.
Akwai abubuwa na rashin jin-dadi wadanda suka far wa Duniya bakidaya, cikin waccan Shekara da ta gabata ta 2020, wato cutar Korona Bairos “Cobid-19”.
Babu shakka, al’umar Duniya bakidaya, ba za ta taba mantawa da mummunan kasgaro da ta fuskanta ta mabanbantan fuskoki, a sanadiyyar barkewar sabuwar annobar cutar ta Cobid-19, da ta mamaye Duniya cikin kankanin lokaci a cikin Shekarar da ta gabata ta 2020.
Hakika daukacin nahiyoyin Duniya bakidaya, sun karbi hisabinsu ne da hannun hagu cikin Shekarar ta 2020, sakamakon waccan annobar cuta ta Cobid-19. Duba da mabanbantan fuskokin rayuwa da cutar ta kassara. Misali, harkar lafiya, harkar tattalin arziki da makamantansu, sun shiga tasku ne a sakamakon bayyanar cutar ta Korona.
Mabanbantan nahiyoyin Duniya da daidaikun manya da kananan Kasashen Duniya, sun hadu da abubuwan dadi, da kuma akasin haka, a cikin Shekarar da ta gabata ta 2020. Misali, babban abin kunyar da ya afku a siyasance da kuma Dimukradiyyance, tattare da Zaben Shugaban Kasa da a ka yi cikin Kasar Amurka, a Shekarar da ta gabata ta 2020.
Da daman Kasashen Duniya, musamman wadanda suka yi imani da tsarin mulki irin na Dimukradiyya, sun matukar shiga tasku gami da zullumi, duba da tutsun da shugaban Kasar mai-barin-gado, Trump, ya tasamma yi, da sunan bai yarda cewa abokin hamayyarsa, Baden, ya runtuma shi da kasa ba a zaben shugaban Kasa da aka gudanar a Kasar. Shugaba Trump, ya kira Zaben da aka yi cikin Shekarar ta 2020, da sunan maras inganci, wanda aka tafka magudi a ciki. Wannan ikirari na Trump, ya matukar sanyaya gwiwar masu bin Kasar ta Amurka sau da kafa, wajen yin koyi da ita dare da rana, tare da fatan taddo ta a fagen kwarewa a siyasance.
Kururuwar da Amurkan ke yi dare da rana, na yunkurin tursasa Kasashen Duniya, na su aiwatar da sahihan zabuka a Kasashensu, sai ya nemi rasa karsashin da yake da shi a idon Duniya, cikin Shekarar ta 2020, duba da bahilar da ta turnuke a tsakaninsa da sabon shugaba mai jiran gado, wato Baden. Ke nan, ita kanta Dimukradiyyar, ta gamu da mummunan mikin da a ka jima Shekara da Shekaru ba a gani, ko ma tunanin afkuwarsa ba, a cikin Shekarar da aka yi ban-kwana da ita ta 2020 a Kasar Amurka.
Ba a nahiyar Latin ba kawai, hatta ma a nahiyar Afurka, tsarin na Dimukradiyya ya samu shaka, a cikin Shekarar da ta gabata ta 2020, duba da irin tarin rigingimun da suka dabaibaye tsarin a Kasashe irinsu Libya da Mali, inda har sai da Sojoji suka amshe mulki daga halastacciyar gwamnatin farar hular da al’umar Kasa suka kafa da gumin goshinsu.
Kasar Nijeriya ma ba za ta zamto waren-gwanki ba, wajen haduwa da nata irin matsaloli a cikin Shekarar da ta gabata ta 2020. Matsalar tsaro; matsalar rashin aikin-yi ga matasa; matsalar durkushewar tattalin arzikin Kasa; durkushewar sabgar ilmi da makamamtansu, sun nemi nunkuwa ne ma a cikin Shekarar da ta gabata, wato Shekarar 2020, sama da yadda suka saba afkuwa a Shekarun da suka gabace ta.
Mummunar yajin-aiki da Kasar ta Nijeriya ta fuskanta daga tsagin Malaman Jami’a na kusan Watanni tara (9) cikin Shekarar ta 2020, shi kadai, ya isa zama shedar cewa, Kasar ba ta girbi alheri ba a fannin ilmi, a Shekarar da aka yi sallama da ita, ta 2020.
Mummunar rashin aikin-yi ga Matasan Nijeriya da ya rika ninkuwa a Kasar, cikin Shekarar ta 2020, yanayin, ya zamto mai matukar razani ne ga masu bincike, masu jin labarai, hatta ma ga kowa da kowa, duba da irin mummunan sakamakon da rashin aikin-yin ya rika samarwa a bangaren tabarbarewar tsaron Kasar. A kullum hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, na matukar nuna damuwa gami da kaduwa ne a cikin Shekarar ta 2020, sakamakon tashin gwauron zabin da yanayin zaman-dirshen ya rika samarwa rukunin matasan Nijeriya, musamman “ya”yan talakawa marasa farcen-susa ko galihu a Kasa.