Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Hannunka Mai Sanda

Fatan Alheri A Sabuwar Shekarar Miladiyya Ta 2021 (II)

by Muhammad
January 8, 2021
in Hannunka Mai Sanda
3 min read
Shekarar
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Bazuwar Ayyukan Ta’addanci Da Afkuwar Rikice-Rikice A Kasa

Babu shakka masu bincike sun kwana da sanin cewa, cikin duk Kasar da ake fama da kamfar ayyukan-yi musamman ga matasa, ayyukan ta’addanci iri-iri ne za su ke biyo baya tamkar tsinkakken carbi, wani bayan wani.

samndaads

Hakika ayyukan ta’addanci da sauran rigingimu sun kara samun gindin zama ne cikin Kasar ta Nijeriya musamman cikin Shekarar da ta gabata ta 2020. Tun da shugaba Buhari ya amshi mulki daga shugaba Jonathan a Shekarar 2015, Zaurukan Majalisun Kasar ba su taba tasamma neman tutse shi ba, saboda matsalar tsaro da ta addabi Kasar, sai a cikin Shekarar ta 2020. Tun bayan sace ‘yan matan Chibok na lokacin gwamnatin PDP, ba a sake haduwa da mummunar garkuwa da daruruwan mutane a lokaci guda ba, irin yadda ya rika faruwa a cikin waccan Shekara ta 2020 da ta gabata.

Cikin Shekarar 2020 ne, bayan shugaban Kasa Buhari ya je hutun Mako guda gida Daura, masu yin garkuwa da mutane su ka bi shi har jihar tasa ta haihuwa, su ka kamfaci daruruwan yara ‘yan makaranta, da sunan an yi garkuwa da su.

Wancan zanga-zanga, ta sai an kawo karshen SARS, ta yi sanadiyyar tafka mummunar asarar dimbin dukiyoyin biliyoyin nairori cikin wasu biranen wannan Kasa, inda wasu bata-gari su ka rika bi waje-waje su na balle shagunan daidaikun mutane da kuma ma’ajiyar hukuma, su na arcewa da su.

Bukatar Yin Hobbasa Daga Hukumomi

Babu shakka akwai matukar bukatar hukumomin da abin ya shafa, tun daga matakin kananan hukumomi, jiha zuwa ga Kasa, ya zamana sun tashi tsaye ne haikan, wajen sanya abubuwa bisa sirdi, ta yadda al’umar wannan Kasa za su yi shirin girbar alhairai a cikin wannan sabuwar Shekara ta 2021, sama da yadda suka dan girba a cikin Shekarar da ta gabata ta 2020, wadda wasu mutane ke neman fassara ta da “Shekarar Tauraruwa Mai Wutsiya”, duba da irin miyagun tsarmakatan da su ka rika yi mata kuri tsawon lokaci.

Ba wai a na nufin cewa, babu wani alheri da jama’ar Duniya ciki har da Nijeriya su ka girba a Shekarar da ta gabata ta 2020 ba, a’a, ko kadan. Sai dai mummunar razani da firgici, durkushewar tattalin arziki da mummunan yanayin talauci da a kullum ke sauya salo wajen yi wa mutane kofar-rago, su ke sanyawa ake gaza ganin ‘yan alhairan da ake dan girba cikin cokali nan da can.

Wadanne kyawawan tanade-tanade ne hukumomi su ka yi wa al’umar Kasa a cikin Kasafin Kudi na wannan Shekara ta 2021?. Wane kaso ne a ka warewa muhimman bangarori irinsu lafiya, ilmi, tsaro da bangaren samar da ayyukan-yi ga matasa?.

Babu shakka, idan ya kasance ba a yi wasu kyawawan tsare-tsaren tallafawa jama’ar Kasa ba, irin yadda hukumomin wannan Kasa ke ta kwakwazon za su yi, ko su na yi, ba abin mamaki ne ba a koma “yar-gidan-jiya, wadda ko kadan ba ma fatan afkuwar hakan. Sannan, yaya wakilcin da mabanbantan hukumomi ke sanyawa wajen tafiyar da ayyukan al’uma? A na sanya hazikan mutane ne bisa muhimman ayyukan Kasa, misali tsaro? A duk sa’adda aka tasamma sanya zalamammu malalata dodaddu bisa jagorantar zarafin tsaro a Kasa, to fa duk irin mamakon biliyoyin kudaden da za a antaya cikin sabgar, kwalliya ba za ta taba biyan kudin sabulu ba.

Shin, bangaren ayyukan lafiya, lantarki, fetur, kwangiloli na gwamnati, a na dankawa ne a hannun masu amana, ko kuwa a hannun ‘yan’uwa da abokai marasa cikakken ilmi da kan-gado ne ake jibinta lamuran? Yaya tarihin rikon amanarsu yake gabanin tsintar kansu bisa kujerun iko a yau?. Idan babu irin wannan bibiyar, duk Duniya, duk irin tsarkin zabe da aka gudanar, to ba za a girbi alheri ba a gwamnatacce, za a yi ta yin tsalle ne a waje guda!!!. Allah Ya kiyashe mu tufka da warwara!!!

SendShareTweetShare
Previous Post

Ronaldo Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare

Next Post

Mutane Ba Su Da Hakuri A Gyaran Jiki, Sun Fi Son Sha-yanzu-magani-yanzu – Rabi Sule

RelatedPosts

Haduran

Batun Yawaitar Haduran Ababen Hawa A Nijeriya (II)

by Muhammad
6 days ago
0

Kididdigar masana na cewa, a duk Shekara a Nijeriya, akalla...

Ababen Hawa

Batun Yawaitar Haduran Ababen Hawa A Nijeriya (I)

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Saboda yau da gobe, sai ya zamana cewa, ba mutane...

Kasafin 2021: Ya Takura Ilimi Da Kiwon Lafiya

Kasafin 2021: Ya Takura Ilimi Da Kiwon Lafiya

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

Inganta tsarin ilimi da kiwon lafiya su ne abubuwa mafi...

Next Post
Gyaran Jiki

Mutane Ba Su Da Hakuri A Gyaran Jiki, Sun Fi Son Sha-yanzu-magani-yanzu – Rabi Sule

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version