Fatanmu Hadin Kan Jama’ar Dutsenwai — Magaji Mai Kwando

Daga Idris Umar,Zariya

A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar ci gaban garin Dutsenwai Alhaji Magaji Mai Kwando ya bayyana manufar kungiyarsu ga manema labarai a yayin da suka kai ziyara sada zumunci a garin na Dutsenwai da ke karamar Hukumar Kubau jihar kaduna.

Alhaji Magaji ya fara godiya ne bisa ganin yadda tawagar manema labaran suka sadaukar da lokacinsu don kawai zuwa gare su don sada zumunci da jin ko wani hali kungiyar tasu mai dauke da tarihi take ciki a wannan lokacin da gwamnti ke bukatar shawarwarin kungiyoyi masu zaman kansu don samar da kyakyawar tsari da wakilci mai amfani ga al’umma.

Baya ga farinci ya ci gaba da bayyana takaitaccen tarihin kungir tasu inda ya ce, a kalla  ta kai shekara 50 da kafuwa domin da yawan mambobin kungiyar sun zo ne sun ganta da ranta tana tafiya.

Kuma ya bayyana manufar kungiyar Inda ya ce an kafatane don kawo ci gaba a fadin karamar hukumar ta Dutsenwai wanda a haka muke a halin yanzu .

Haka kma shugaban ya zayyano abubuwan alheri da kugiyar take aiwatarwa a fadin garin na Dutsenwai da kewaye. Daga ciki akwai hadinkai da suka samu da duk masu fada aji na wannan gari, sannan kuma ya bayyana cewa har yanzu akwai cikakken hadinkai tsakanin matasa da ya sa ba a samun wata Matsala a tsakanin juna, ya ce wannan a garesu abin lurane, shugaban ya bayyana cewa har yanzu ba su bar gudanar da aikin gayya ba da ya shafi gyran titi wato ko a makon daya gabata sun sayo tifofin kasa da kudinsu sun cike wasu ramuka a cikin garin na Dutsenwai ya ce ba a dade ba kungiyar ta gyara layin wutar lantarki da suka sami matsala Kuma ya bayyana yadda suke taimakawa yan’uwansu matasa in abin taimakon ya taso,kuma yace a yanzu kan manyansu a hade yake kuma suna basu goyan baya akan duk abin da ya taso ya kare da cewa sanada tsaretsare na samawa matasa aikinyi don samun dogaro da kai wandannan sune kadan daga cikin abinda shugaban ya zayyano dake nuna yadda kungiyar tasu take tafiya.

Alhaji Magaji ya kuma bayyana burin kugiyar na samar da hadin kai da zaman lafiya a garin nasu baki daya.

Shi kuwa Farfesa Muhammad Kabir Aliyu na jami’ar Ahmadu Bello ta zariya ya tabbatar da kokarin da kungiyar take yi a matsayinsa na tsohon shugaban kungiyar a shekarun baya kuma ya yaba kwarai da gaske tare da basu shawaran dagewa da baiwa matasa shawaran komawa karatu Inda shi farfesan yayi masu alkawarin duk matashin da ya sami takaradar shiga jami’a to zai mashi tallafi na musamman tuni kuma har ya fara Lamar yadda bicike ya nuna.

Daga karshe shugaban ya yi amfani da wannan dama ya mika godiyarsa ga daukacin iyayen su musamman sarakuna da jami’an tsaro da masu hannu da shuni dake ciki da wajen garin da suke basu goyan baya ta bangarori da dama yace Allah ya taimaki jihar kaduna da karamar Hukumar Kubau da jama’ar cikinta baki daya.

Exit mobile version