Fatawar Kashin Dankali

Masallacin Shehi Alhamza da ke Unguwar Dubarudu, na yawan cika ya batse a duk yayin da aka fara Tafsirin Azumi. Daga mahalarta wajen wa’azin Shehin, za a ga sun haɗar da; talakawa; masu hannu da shuni; da uwa-uba masu riƙe da madafun-iko.

A wata Laraba da yamma bayan ƙare Tafsiri, sai wani ya yi tambaya cewa, “Shin Shehi, mene ne hukuncin mutumin da fitar da Zakka ya wajaba a kan sa amma ya yi mursisi ya ƙi fidda wa?”. Ko da Shehi ya yi ƙoƙarin amsa tambayar, yana duba dama gare shi sai ya yi kwalli da Alhaji Cinnaka, nan da nan Shehin ya mai da ganinsa gabansa, nan ma sai ga Alhaji Damamusau ya yi masa ƙuri-da-idanu. Yana da kyau mai karatu ya sani cewa, waɗannan ƙasurgumayen masu kuɗi biyu da suka yi tirkoko a gaban Malam, kakaf a nahiyar, babu wani mahaluƙi da ya kama ƙafarsu wajen ƙarfin tattalin arziƙin aljihu. Sai dai kash! Duk banbaɗancin wani mai banbaɗanci, bai isa ya ce tsakanin Alhaji Cinnaka da Alhaji Damamusau ɗayansu ya taɓa fid da Zakka ko da kuwa sau guda ba.

Mai yi wa, kasantuwar Shehi na tsaka-mai-wuya ne game da amsa waccan tambayar, kawai sai a ka ga ya hau wani banbami kamar haka, “Shin ya Ilahi, me ya sa mutanen yau ba sa neman sauƙi wurin Mahaliccinsu ne! Yana da kyau mu sani cewa, Shirka da Allah ne kaɗai laifin da aka faɗa a wurare da dama cewa Allah ba ya gafartawa Bawa. Don Allah “yan’uwa musulmi mu kau da ƙyashi da hassada daga ƙirazanmu, sai mu tsarkaka. Mu gusar da ɗabi’ar son danna ba’arin (sashen) ‘yan’uwanmu musulmi cikin wutar Jahannama ta ƙarfi. Allah dai ya shirye mu”.

Mai tambaya na biyu ya ɗora kamar haka, “Allah Shi gafarta, yaya lamarin Shugaba Azzalumi ke kasancewa ne a ranar tsaiwa gaban Allah?” Nan fa Shehi ya gyara zama, ya fid do wani gajeren tsanwan hankici daga aljihun “yar-cikinsa ɓarin hagu, ya sharce wani gumi da ya malalo masa yanzun nan daga tsakiyar goshinsa zuwa fuskarsa da kumatunsa biyu. Ko da na ji, ashe zancen nan da ake, mutane huɗu ne kacal tsakanin sa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwanare, wanda ko cikin makon da ya gabata ya kawo Bahuna ashirin na Shinkafa Masallacin don a kasaftawa mabuƙata: kuma ya ba da alfarmar kujerun Umarah huɗu, a bai wa Liman biyu, na’ibi ɗaya, saurar kujerar guda kuma a bai wa Maja-baƙi.

Bayan Shehi ya numfasa, sai ya amsa waccan tambaya kamar haka, “A gaskiya fa ba Shugabanni ne matsalarmu ba a wannan lokaci kamar yadda akasarin ammawan mutane ke guna-guni, Waziransu ne babbar illar da ke dabaibaye al’amura. Ba ku ji ma Malam Bahaushe na cewa ba a mugun Sarki sai mugun Bafade. Shi Shugaba, tamkar ciki-lafiya ne baka-lafiya. Ina fata an fahimta. Saboda haka, wajibin mu ne mu riƙa kyautatawa Shugabanni zato, muna yi musu addu’ar gamawa lafiya. Yin hakan, shi ne ɗabbaƙa addini gangariya.

Mai tambaya na uku ya ce, “Don Allah, me Shehi zai ce game da Talaka mai nacin maula ga jama’a?”. Cikin fushi Shehi ya amsa da cewa, “Yawwa! Ka ji cikakken Shaiɗanin, maras godiyar Allah, wanda za ma ka iya kwatanta shi da Kare ta wata fuskar. Eh mana! Ai duk mai irin wannan ta’adar za a same shi maras zuciya, tun da wani zai ba shi, wani ko ya ɗaure masa fuska ya hana shi. Amma ɗan-farka haka zai koma gobe tsamo-tsamo. Ya al’umar musulmi, mu fa sani cewa, duk mai mayar da roƙe-roƙe a matsayin sana’a, akwai wani Hadisi Sahihi da ke nuni da cewa, zai bayyana ranar Lahira tamkar KWARANGWAL, ɗaukacin shacin fuskarsa babu nama ko na KWABO.

Mai tambaya na huɗu ya ce, “Allah Ya ja kwanan Malam, shin mene ne sakamakon mai yin FATAWAR KASHIN DANKALI a MUSULUNCI?”. Nan fa Shehi ya ɗora da, “Sai wanda ya tumbatsa ƙirjinsa ya cika da ilmi fanni-fanni ne kaɗai zai iya kai ga fahimtar cewa an yi Fatawar Kashin Dankali ko ba a yi ba, amma ba gama-garin mutane ba”.

Gama ba da wannan fatawa ke da wuya ne, Shehi ya ankare jama’a sun fara guna-guni cikin Masallaci. Nan da nan Malam ya ce, “Bisirril Faaaaaaatihaaaaaa! Ko da aka kaure da karatun Fatihar, sai Liman ya kara wayarsa a kunne tamkar yana amsa waya ne ya fice cikin hanzari daga Masallacin. A wannan rana dai maja-baƙi ne ya yi addu’ar HATAMA.

Mutari Anwar

0803 667 9084

 

Exit mobile version