Ammar Muhammad" />

Fayemi Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya

Ekiti

A daren jiya Laraba aka zabi sabon shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya wato NGF, inda kungiyar ta zabi Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi. Gwamnan ya zama shugaban kungiyar ne bayan samun amincewar sauran ‘yan takarar da ke neman shugabancin kungiyar lokacin taron da kungiyar ta yi a Abuja.

Gwamna Kayode, zai maye gurbin Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, wanda ya jagoranci kungiyar daga shekarar 2015.

Kungiyar ta zabi Gwamnan Sakkwato Aminu Tambuwal, a matsayin sabon mataimakin shugaban kungiyar, wa’adin su zai fara daga shekarar 2019 zuwa 2021.

Exit mobile version