FCTA Ta Kafa Kwamitin Mutum 20 Don Tsaftace Birnin Abuja

A kokarnta nan tsaftace birnin Abuja da kewaye, Hukumar raya babba birnin tarayya (FCTA), in ta kafa kwamiti mai mutum 20 don fito da tsarin birnin da kowa zai yi alfahari da shi. Wannan shirin na caga cikin tsarin da masu ruwa da tsaki ne suka fito da shi don samar da tsaftaccen gari day a kauce wa dukkan matsaloli.

Da ya ke kaddamar da kwmaitin mai dauke da mutum 20, Ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya ce, “Dukkan birane kamar halittu yana munfashi ya na wahala yana rashin lafiya in har ba a yi cukaken lura das hi ba, zai kuma iya lallacewa gaba daya.”.  ya yi korafin cewa, yawancin birane a fadin duniyar nan musamman a kasashe masu taso wa suna fada a matsala I dan aka kasa tsara su, yawancinsu sun fada matsaloli kala kala, kamar samun mattara talakawa da kuma samun gine gine babu ka’ida, wannan lamarin kamar kansa ne in har ba aiya maganinsa ba zai iya kai wa halin da ba za a iya maganinsa ba”.

‘Yan kamitin da aka kafa sun hada da, babban sakataren Hukumar raya babban birnin tarayya Abuja FCDA, Injiniya Umar Gambo Jibrin a matsayin shugaba sai shugaban kungiyar UN-Habitat a Nijeriya, Malam Kabir Yari, sai kuma wani sanannen dan radin kare muhalli, Dakta Limota Goroso-Giwa, da sauran masana daga bangarorin ryuwa daban daban da kuma wakilai daga kungiyar ‘yan asalin yankin Abuja.

A jawabinsa na maraba a ajen taron, sakataren dindin na yankin Abuja, Sir Chinyeaka Ohaa, ya ce, ya zama dole ga ‘yan kwamitin su yi aiki kafada da kafada da wadanda suka kikiro shirinb tun da farko wato ‘Huairou Commission’ don a samu nasara day a kamata a dukkan lamarin.

Ya kuma yaba wa ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello a bisa kokarinsa na ganin an samu gari mai tsafta wadda za a iya alfahari das hi a dukkan fadin duniya.

Da yake tsokaci a wajen taron, Sakataren hukumar FCDA, Ininiya Jibrin, ya yi alkawarin cewa, kwamitin za ta yi iya kokarinta na sauke nauyin da aka dora musu.

Exit mobile version