Fellaini Ya Yanke Shawarar Barin Manchester United

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Maroune Fellaini, ya bayyana cewa, ya yanke shawarar barin kungiyar a karshen kaka mai kamawa, bayan da kwantaraginsa zai kare a kungiyar cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.

Fellaini, mai shekara 30 ya koma Manchester United ne daga kungiyar kwallon kafa ta Eberton a shekarar 2013 shekarar da tsohon mai koyar da kungiyar Dabid Moyes, ya karbi aikin kungiyar ta United bayan ritayar Sir Aled Ferguson.

A wannan kakar Fellaini ya sha fama da ciwo inda ko a yanzu yana jinya bayan rauni da ya samu a wasan kungiyar, kuma zai shafe kusan watanni biyu yana jinya kafin ya dawo ci gaba da bugawa kungiyar wasa.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar, Jose Mourinho, ya bayyana cewa dan wasan yana da amfani a kungiyar wanda hakan ya sa kuma ba za su yarda su rabu da dan wasan ba.

Sai dai dan wasan ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar sakamakon rashin buga wasanni akai-akai a kungiyar, inda tuni ya yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Basiktas dake kasar Turkiyya domin ci gaba da buga wasaninsa a kungiyar.

Tuni dai kungiyar ta fara neman dan wasan da zai maye gurbinsa a karshen kaka mai kamawa.

 

Exit mobile version