Fernandez Ya Zama Gwarzon dan Wasan Manchester United Na Bana

Daga Abba Ibrahim Wada

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kungiyar na shekarar bana na wanda yafi kowa kokari a kungiyar a kakar bana mai karewa.

Karo na biyu kenan a jere da dan wasan ke lashe wannan kyauta duk da cewar a watan Janairun shekara ta 2020, ya kulla yarjejeniya da Manchester United daga kungiyar Sporting Lisbon ta Portugal.
Cikin sanawar da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, Manchester United ta ce Bruno Fernandez ya lashe kyautar gwarzon nata na bana bayan samun mafi rinjayen kuri’un da magoya bayan kungiyar suka kada daga kasashe fiye da 200, abinda ya bashi nasarar doke dan wasan gaaba, Edinson cabani da kuma Luke Shaw.

A wannan kakar wasa, kwallaye 18 gwarzon na Manchester United ya ci cikinsu har da guda 9 a gasar Europa, ya yin wasanni 36 da ya buga kuma har yanzu ba’a kammala buga wasan kakar bana ba.

A ranar Lahadi Manchester United zata fafata da kungiyar kwallon kafa ta Woberhampton a wasan kungiyar na karshe sannan kwanaki uku tsakani ta buga wasan karshe na cin kofin Europa League da billareal a birnin Gdansk na kasar Poland.

Exit mobile version