Abubakar Abba" />

Fetur Ya Sauka Zuwa Dala 46, Cewar OPEC

Matakin mai na kasa da kasa, (Brent) danyen mai, ya fadi Dala 46 a ranar Juma’a, yayin da tattaunawa ta gudana tsakanin kungiyar kasashen dake Fitar da Man Fetur da takwarorin.

Rasha da Shugabanin kawancen 10, ta nuna rashin yardarta game da wani shiri na samar da gurbataccen mai don magance tasirin cutar Coronabirus kan bukatun mai na duniya, majiyoyin dake cikin tattaunawar sun fakawa S&P Global Platts, cewa Brent, yana fuskantar koma baya tun lokacin da coronabirus ya barke, man ya fadi da Dala 3.84 zuwa Dala 46.15 a kowace ganga da misalin karfe 8:10 na dare agogon Nijeriya.
A ranar Alhamis din nan ce OPEC ta bayyana wani shirin da zai karkatar da samar da adon kudade ta karin ganga miliyan 1 a kowace shekara, wanda zai dogara ne ga Rasha da sauran kungiyoyi tara wadanda ba OPEC ba, da ke da aniyar kawar da nasu ta hanyar bpd 500,000 .
Amma yin amfani da shi don yin kasuwanci a kansa, kasar Rasha ta yanke hukuncin cewa yin haka kamar an nuna gazawa ne. Ministan Makamashi na Rasha, Aledander Nobak, ya tsaya kai da fata cewa, ya kamata kungiyar ta jira har sai lokacin taronsu na watan Yuni don yanke hukunci game da duk wasu abubuwan da za su kara samar da kayayyaki masu zurfi, tunda duk wani motsi na wucin gadi yanzu ba zai yi tasiri a kasuwar ba.
A cewar rahoton, matakin na Rasha ya firgita da yawa daga mambobin kungiyar OPEC, musamman Saudi Arabiya, wadanda ke kara matsin lamba don sanya karfin kasuwa a kokarin kawancen don shawo kan matsalar lalacewar cutar Coronabirus.
Ministocin sun shafe safiyar Juma’a a wani hadaddiyar zazzafar tattaunawa da bangarori da yawa, tare da jinkirta taron OPEC + na minista daga lokacin da aka shirya shi da misalin karfe 10 na safe (0900 GMT) na sama da awanni shida.

Exit mobile version