Kungiyar Lauyoyi mata na kasa da kasa wato (FIDA) tare da hadin gwiwar gidauniyar Ah-Muhibbah Foundation sun ‘yanto Fursunoni guda 15, inda mutum sha hudu suka kasance maza da kuma wata mace guda daya daga gidan yarin Suleja.
Gidauniyar Al-muhibbah dai na matar gwamnan jihar Bauchi ce, Hajiya Aisha Bala Muhammad wacce ta assasa da zumbar gudanar da ayyukan taimakon al’umma a fadin kasar nan.
A yayin da take mika rasidin biyan kudin tara na wadanda suka ‘yanto ga shugaban gidan yarin, shugaban kungiyar mata Lauyoyi FIDA reshen birnin tarayya Abuja, Misis Racheal Adejoh Andrew, ta shaida cewar kungiyar ta damu da cinkoson Fursunoni a gidajen yarin kasar nan lura da yadda annobar Korona ke kara bazuwa.
Ta ce a bisa hakan ne suka himmatu wajen lalubo bakin zaren magance matsalolin ta hanyoyin da za su iya.
“Duk da ya ke babu mata da yawa cikin jerin wadanda suka ci gajiyar wannan sa’ayin namu, amma mun sani al’ummomi su na wanzuwa ne ta hanyar maza da mata, kuma su mazan suke sa’ayin kula da iyayensu mata, matayensu na aure, kannensu, yayunsu mata, ‘yan uwansu. A bisa hakan ne ma muka kasance a nan.”
Ta nuna cewa kuma da ya ke babu daurarrun mata da yawan, sun zabi fito da zama 14 da kuma mace 1 domin ba su damar komawa ga iyalansu tare da cigaba da harkokin rayuwa kamar kowa.
A jawabinsa shi kuma, shugaban da ke kula da gidan yarin na Suleja, Abdulrahman Musa, ya nuna matukar farin cikinsa a bisa kokarin da FIDA suka yi tare da irin wannan tallafin da suka yi na fitar da wasu daurarrru a gidan.
Ya ce, cinkoson mutane a gidan yarin na daga daga cikin muhimman kalubalen da suke ci musu tuwo a karya, yana mai cewa an samar da wannan gidan yarin ne da tsarin yake cin mutum 250 a lokaci guda, amma yanzu sama da fursunoni 761 ke rayuwa a ciki.
Ya shaida cewar ta irin wannan hanyar na biyan kudin tara da aka yanke ma wasu, zai yi gayar taimakawa wajen rage cinkoson daurarru a gidajen yarin kasar nan.
Bayan fitar da fursunoni 15 din, kungiyoyin biyu sun kuma rabar da tallafin kayayyakin tafiyar da rayuwa na yau da gobe ga fursunoni mata da kananan yaransu.