Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bukaci a maimaita wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da aka fafata tsakanin Afrika ta kudu da Senegal bayan samun alkalin wasan da yin coge.
FIFA ta dakatar da Alkalin wasan dan Ghana Joseph Lamptey har abada bayan ya yi coge a alkalancin wasan da Afrika ta kudu da Senegal suka buga a watan Nuwamban 2016.
Afrika ta kudu ce ta yi nasara da ci 2-1 bayan alkkalin ya ba kasar wani fanariti da har ya janyo aka dakatar da shi.
Matakin maimata wasan dai yanzu na zuwa a yayin da Senegal ke matsayi na uku a rukuninsu na D a yayin da kuma ya rage wasanni biyu.