Daga Abba Ibrahim Wada
Mai tsaron bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Virgil van Dijk da Mohammed Salah da Sadio Mane da kuma Thiago Alcantara na cikin jerin sunayen ‘yan wasan Liverpool da ke takarar lashe kambun gwarzon dan wasan hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.
Shi ma dan wasan tsakiyar Manchester City Kevin De Bruyne na daga cikin yan wasa 11 da aka rairaye don lashe kyautar ya yinda a bangaren mata kuwa, ‘yar wasan Ingila da Manchester City Lucy Bronze ta samu shiga jerin wadanda ke takarar lashe kambun.
Shi ma mai koyarwa Jurgen Klopp na Liverpool da mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leeds United Marcelo Bielsa sun samu shiga jerin masu horar da ‘yan wasa mafi bajinta a bana.
Za’a fara jefa kuri’ar ranar 25 ga watan Nuwamba har zuwa 9 ga watan Disamban shekara ta 2020, kafin sanar da wadanda suka lashe kyautar a ranar 17 ga watan Disambar a wani biki da hukumar zata shirya
A wani bangaren, kwallon da dan wasan gaban Tottenham Son Heung-min ya ci Burnley na daga cikin kwallayen da ke takarar mafi kayatarwa da ake yi wa lakabi da ‘Fifa’s Puskas Award’ kuma itama tana cikin wadanda za’a tantance.
A bangaren kwallon mata, ‘yar kasar Scotland Caroline Weir, mai buga wasa a Manchester City, na cikin jerin masu neman Fifa’s Puskas Award din duk da cewa a halin yanzu tana kwance tana jiyya sakamakon ciwon data samu.
Ga jerin sunayen ‘yan kwallo maza masu neman lashe ‘Best Fifa Football Awards 2020’
Thiago Alcantara (Spain, Liverpool)
Cristiano Ronaldo (Portugal, Juventus)
Kevin de Bruyne (Belgium, Manchester City)
Sadio Mane (Senegal, Liverpool)
Kylian Mbappe (France, Paris St-Germain)
Lionel Messi (Argentina, Barcelona)
Neymar (Brazil, Paris St-Germain)
Sergio Ramos (Spain, Real Madrid)
Mohamed Salah (Egypt, Liverpool)
Virgil van Dijk (Netherlands, Liverpool)
Bangaren Mata
Lucy Bronze (England, Manchester City)
Delphine Cascarino (France, Lyon)
Sam Kerr (Australia, Chelsea)
Saki Kumagai (Japan, Lyon)
Dzsenifer Marozsan (Germany, Lyon)
Vivianne Miedema (Netherlands, Arsenal)
Hans-Dieter Flick (Germany, Bayern Munich)
Jurgen Klopp (Germany, Liverpool)
Julen Lopetegui (Spain, Sevilla)
Zinedine Zidane (France, Real Madrid)
Mata masu horarwa
Lluis Cortes (Spain, Barcelona)
Rita Guarino (Italy, Juventus)
Emma Hayes (England, Chelsea)
Stephan Lerch (Germany, Wolfsburg)
Hege Riise (Norway, LSK Kbinner)
Jean-Luc Basseur (France, Lyon)
Sarina Wiegman (Netherlands, Dutch national team