Connect with us

WASANNI

Fifa Ta Yi Min Rashin Adalci,In Ji Griezman

Published

on

DOLE MU DAGE DOMIN LASHE KOFIN KALUBALE — CEWAR KOCIYAN KANO PILLARS

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Ibrahim Musa ya yi kira ga ‘yan wasan kungiyar da cewa dole sai sun rage yawan yin kura kurai a wasa idan har sunason su lashe kofin kalubale na kasa wato Aito Cup.

Kano Pillars dai ta samu nasara a kan kungiyar Ngwa United FC ta jihar Ebonyi a wasan da suka buga a satin da ya gabata wanda hakan ya sa yanzu za su hadu da kungiyar kwallon kafa ta Sakkwato United a wasan zagaye na gaba hakan ya sa kociyan ya ce dole akwai bukatar dagewa.

Mai koyarwar ya ce kungiyar tasamu nasara a kan kungiyar Ngwa duk da cewa sun yi sake har an zura musu kwallaye a raga kuma duk laifinsu ne saboda haka dole sai sun rage yin kura-kurai a wasan da za su fafata da Sakkwato United.

‘Mun yi sa’a mun samu nasara a kan Ngwa United saboda mun yi shirme sun zura kwallaye biyu a ragar mu kuma hakan da muka yi bai kamata ba saboda idan kanason samun nasara dole ka rage kura-kuran da ba su kamata ba” in ji kociyan

Ya ci gaba da cewa “ Dole sai an yi kuskure a kwallon kafa amma kuma dole sai an rage yawan yinsu saboda yanzu duk kungiyar da tazo wannan matakin ba ta yin kuskure da yawa kuma na gayawa ‘yan wasana cewa abinda suka buga a wasanmu da Ngwa bai burgeni ba kuma sai sun sake dagewa”

Ya kara da cewa Sokkoto United ba karamar kungiya bace duba da yadda sune suka doke kungiyar MFM na jihar Legas hakan zai sa su gane cewa ba karamin aiki ba ne a gabansu idan har suna son suga sun samu nasara.

A karshe ya ce ba za su tsaya su ga kungiyoyi suna lashe kofuna ba su kuma suna kallo saboda haka dole sai sun dage sunga yadda suma za su ci gaba da samun nasara.

 
Advertisement

labarai