Abba Ibrahim Wada" />

Fifa Ta Zabi Alkalan Wasanni Mata Uku Domin Alkalanci A Kofin Duniya

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana alkalan wasan da za su ja ragamar gasar Zakarun nahiyoyin duniya wato Club World Cup da za a yi a kasar Katar kuma an bayyana alkalan wasa bakwai da mataimaka 12 da za su gudanar da aikin har da masu kula da na’urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato BAR.

Mata uku da aka zaba sun hada da Edin Albes Batista wadda ta hura wasa a gasar matasa ta duniya ta ‘yan kasa da shekara 17 a Indiya a 2017 da Esther Staubli da kuma Claudia Umpierrez, wadda ta alkalanci wasa biyu a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 da aka yi a Brazil a 2019.

A karshen makon nan ake sa ran dukkan alkalan da aka zabo za su kammala shirye-shiryen gabatar da kansu a Katar, kafin gasar ta kankama haka kuma kasar da za ta karbi bakunci da kuma Fifa za su gabatar da dukkan matakan kariyar yada cutar korona a lokacin gudanar da gasar da ya kamata a buga a badi, amma aka dage saboda bullar annobar.

Ranar 19 ga watan Janairu za a yi bikin raba jadawalin zakarun nahiyoyin da za su kara a tsakaninsu sannan za kuma a fara wasannin a Doha tsakanin 1 zuwa 11 ga watan Fabrairun 2021, inda ake sa ran buga wasan karshe ranar 11 ga watan Fabrairu.

Exit mobile version