Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino ya bayyana mutukar goyan bayan sa ga fadada gasar cin kofin kungiyoyi na duniya nan gaba domin bawa wasu kungoyin damar fafatawa a gasar.
Infantino wanda ya bayyana goyan bayan nasa yayin zantawa a wata hira da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya ce, hakan wata hanya ce ta bunkasa gasar kasa da kasa tsakanin kungiyoyi.
Yana mai cewa maimakon kungiyoyi bakwai da suke wakiltar nahiyoyi, lokaci yayi da ya kamata a kara adadin wanda hakan zai sake kawo hadin kai sannan kuma za’a samu karin kudin shiga a daidai lokacin da duniya take fama da rashin kudi sakamakon cutar Korona.
Yanzu haka ana saran kungiyoyi 24 zasu fafata a gasar ta bana da kasar China zata karbi bakunci ciki har da kungiyoyi 8 daga nahiyar Turai wadanda aka bayyana sune zasu dauki kaso mafi tsoka idan za’a buga.
Sai dai Infantino bai fayyace yadda za’a tsara gasar ba amma ya bayyana cewa yana goyon bayan kiraye-kirayen kuma hukumar Fifa a shirye take data bayar da cikakken goyon bayanta akan sabon tsarin.
Za A Yi Kare Jini Biri Jini Tsakanin Real Madrid Da Atletico Gobe
A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta ziyarci filin...