An bayyana cewa fifita kamfanonin kasashen wajen Nijeriya da kayayyakinsu da ya zama alada ga gwamnatocin kasar nan ga al
ummarta da cewa wani abu ne da zai ci gaba da maida kasar nan mai Albarka baya, mudddun gwamnatocin Tarayya da na Jihohin da sauran Hukumomi masu ruwa da tsaki ba su dauki matakin dakatar da hakan ba.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban kamfanonin rukunin JIFATU na kasa da ke Kano, Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad a lokacin da ya ke zantawa da manema Labarai kan yunkurin da wani kamfanin Afrika ta Kudu da ya bayyana wasu sababbin tsare-tsaran sa da kudirinsa na barin Nijeriya. An gudanar da taron Manama labaran ne a Birnin Kano a ranar Talatar nan da ta gabata.
Alhaji Sabitu ya ce, tun a farko su a matsayin su na masu sadaukar da kai a harkar kasuwanci da alamuran al
umma sun hango cewa dogaro da kamfanonin waje da kayayyainsu ba zai haifar wa da Nijeriya da mai ido ba. Don haka tun da suka fahimci haka suka tashi tsaye suka yi ta fadi-tashi na kafa irin wadannan kamfanoni da za su yi gogayya da na kasashen waje, inda su ka yi yunkurin farko a Birnin Tarayyar Abuja, amma wasu dalilai suka sa aka dakatar da wannan yunkuri suka dawo Kano suka kafa Kamfanin JIFATU.
Ya ce a yanzu haka suna rassa a wurare daban-daban a Jihar Kano, kamar kan Titin Obasanjo da hanyar Zariya, duk cikin Birnin Kano. Haka suka je Zamfara, Katsina, Bauchi, Jigawa, Kaduna da dai sauran su, wanda yanzu haka a Kaduna suna tsaka da aikin samar da kamfanin da ya dace da mutanan wannan yanki, da ma Nijeriya baki daya, za su amfana da irin wannan kamfani.
Har ila yau ya ce, ganin yadda ‘yan Arewa tun a baya aka mai da su kamar ‘yan B0ra, wasu kuma ‘yan Mowa “ya sa na sa daukar da kaina ta hanyar zuba kudade masu yawa domin a gano cewa mu ‘yan Arewa muna da yawa, kuma a hukumomin kasar nan wasu abubuwan su ke faruwa muna kallo da masana suka kammala binciken da muka sa su, sai suka bayyana mana cewa akwai hukumomi masu tasirin gaske, wanda babu ‘yan Arewa a cikinsu, hakan ya sa muka sake wani aikin domin bayyana wa gwamnatin tarayya cewa ga halin da ake ciki, domin ta dau mataki na a ga an daidaita yadda abu ya kamata a zama a Nijeriya”, in ji JIFATU.
Dan kasuwar ya ci gaba da cewa, “saboda haka shawarar mu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da daukacin Hukumomi masu ruwa da tsaki a Nijeriya shi ne su samar da tsarin zakulo duk amfanin gonar da kowacce Jiha ke da shi ta hanyar baje kolin albarkatu gona a matakai daban-daban na kasar nan, kamar matakin Kananan Hukumomi da Jihohi, ta yadda kowacce a gane abun da ta ke da shi a yi tsari na kafa masana’antu na sarrafa irin wadannan abubuwa na albarkatun gona, kamar irin su Ridi , Gyada, Wake, Shikafa, Acca, Iburu, Masara, Dawa, da dai sauran albarkatun gona da Allah ya ba mu a Najeriya.”
Haka Zalika ya ce, tsarin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi akan takin Zamani na sama kamfanoni ido da aka yi yarjejeniya da su da kuma tsarin da akai da su na wadata taki a kasar nan, to haka ya kamata a yi na samar da kamfanonin kasar nan.
“Kuma ya kamata a ce mu yi amfani da damar mu, duk da ba murna mu ke yi da barin wani kamfanin waje daga Nijeriya ba, amma abin da ya kamata, tun da haka ta faru, to mu yi amfani da wannan damar wajen samar da kamfanoni, tare da ba su shawarwari na ci gaban kasuwancin zamani da na shari`a da dai saursn su,” in ji shi.
A karshe Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad ya yi kira da Gwamnonin kasar nan da sauran hukumomi, musamman Gwamnonin Arewa da Su yi koyi da Gwamnan Zamfara, wanda ya yi alwashin cewa duk abin da Gwamnati za ta saya, to a Zamfara za ta saya, kuma duk inda yake sayen kayan bukatunsa na yau da kullum ba zai canza ba, kuma a haka a ke. Wannan ya farfado da tattalin arzikin ‘yan zamfara da ma masu hulda da su a Nijeriya.