Filato ta tsakiya ta amince da tazarcen Gwamna Caleb Mutfwang a wa’adi na biyu a zaben shekarar 2027.
Amincewar ta biyo bayan abin da masu ruwa da tsaki suka bayyana a matsayin shugabancinsa na kishin jama’a da kawo sauyi, wanda ya yi tasiri sosai a birane da kauyuka a fadin jihar.
- Mutane 10 Sun Rasu, 29 Sun Ɓace A Mummunan Hatsarin Jirgin Ruwa A Sokoto
- Yadda Arsenal Ta Doke Manchester United Da Ci 1-0
An cimma matsayar ne a yayin wani gagarumin taron masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin jam’iyyar, shugabanni da jiga-jigan siyasa na shiyyar, wanda aka gudanar a Retnan Suites, Jos.
Shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar ta tsakiya Hon. Monday Daspan, wanda ya shirya taron, ya ce Gwamna Mutfwang ya daga darajar mulki a Jihar Filato ta hanyar shugabanci na musamman da ya sa ‘yan jihar ke matukar kaunarsa.
Ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru biyu kacal, gwamnan ya dauki kwakkwaran matakai na ci gaba, wadanda suka mayar da jihar kan turbar ci gaba mai dorewa. Ya bayyana gwamnan a matsayin “Kyautawar Allah ga Filato, wanda aka aiko domin ya farfado da sake gina jihar bisa hangen nesa na iyayen da suka kafa ta.”