In dai ana maganar tafiya-tafie musamman masu dogon zango, to dole ana buƙatar jiragen sama, wanda ita ce tafi sauri wajen kai matafiyi inda za shi.
Sai akwai matsala ta ƙarancin tituna na saukar jirage waɗanda ba su da yawa a wasu wuraren. Ma’ana a nan, dole ne matuƙin jirgin sama ya kasance yana da cikakkiyar ƙwarewa don ya samu damar iya sauka a kan titin jirgi ko akan wani tsauni da ke da gangarara. Duba da yanayin halin da wasu filayen jirgi suke ciki, mun ɗaƙulo guda 10 waɗanda suka fi haɗari musamman yayin sauka:
Filin Jirgin Lukla
Filin Jirgin Courcheɓel A Faransa:
Filin sauka da tashin jirage na ƙasa na Courcheɓel da ke ƙasar Faransa, shi ma yana ɗaya daga cikin filayen jiragen 10 masu wahalar sauka. Faifan bidiyo da ke kula da sauka da tashin jirage a titin jirgin, a shekarar da ta wuce ce ta samu matsala, inda hakan ya kawo matsala sosai wajen saukar jiragen. Har ila yau. tsawonsa bai fi mita 525 ba. Banda wannan kuma, titin ya ragu da kashi 18.5 bisa 100, inda hakan yake zamowa matsala ga tashin jirage daga filin.
Wani ƙari akan wannan matsalar kuma ita ce, titin saukar jiragen an gina shi ne yadda dole matuƙi ya sai ya bi ta kan hanyar rafi kafin ya sauka ko ya tashi. Idan kuma jirgi bai samun isasshen gudu kafin ya tashi daga kan titinsa ba, komai yana iya faruwa.
Kamar yadda aka sani, filayen jiragen sama da ke tsakanin tsibirai suna wahalar da matuƙin jirgi idan zai tashi ko kuma ya sauka. Filin sauka da tashin jirage na Toncontin shi ma yana ɗaya daga cikin waɗannan filayen sauka da tashin jiragen sama. Idan jirage suna son su yi tashi ko saukar da ta dace, dole ne matuƙi sai sun yi gudu na tsawon zango 45 don su tashi daga kan titin saukar jiragen.
Bayan wannan kuma, jiragen dole ne su tashi da sauri tare da kiyayewa, don kada su samu matsala wajen tashi ko sauka.
Filin Jirgin Princess Juliana:
Filin jirgi na Princess Juliana, shi ma sananne a cikin jerin waɗanan filayen jiragen na duniya masu haɗarin gaske.
Titin saukar jiragen kusa yake da wani babban Rafi, inda hakan ke haifar da ƙarar jirage da kuma tashin ƙura ga waɗanda suka je gindin Rafin don shaƙatawa. Titin saukar jiragen bai wuce tsawon mita 2,179 ba, wanda ya yi matuƙar ƙanƙanta, idan aka yi la’akari da girman babban jirgi dake buƙatar sauka akan titin jirgin sama mai tsawon sama da mita 2,500 don sauka cikin nasara.
Filin jirgin na Princess Juliana tunda farko an gina shi ne don sauka da tashin ƙananan jiragen sama, amma saboda bunƙasar zuwa yawon buɗa ido, har jirage ƙirar A340s da kuma ƙirar 747s suna sauka a filin jirgin.
Filin Jirgin Ƙasar Gibraltar:
Titin saukar jirage na wannan filin Jirgin ba shi da matsala sosai. Wani abin sha’awa shi ne, an zana shi ne yadda sigoginsa ke haifar da matsala wajen sauka a kan shi. Babban titin dake yankin Winston Churchill wanda ya ratsa ta kan titin saukar jiragen dole ne sai an rufe shi idan jirage za su sauka.
Ba dukkan mutane ne suke yin tafiye-tafiye a wannan filin jirgin ba saboda ƙarancin kayan aiki. Titin sauka da tashin jiragen ba gajere ba ne, amma an yi shi ne da dusar ƙanƙara wanda ke bawa jiragen damar sauka. Sai dai a wasu lokutan ana gamuwa da ƙalubale yayin saukar jirgi.
Ma’aunin yanayi na filin jirgin yana yana haifar da sanyi har na tsawon shekara. A shekarar 1970, akwai jirgin sama ƙirar C-121 da ya yi haɗari wanda har yanzu yana bizne cikin dusar ƙanƙarar. Watanni da dama da suka wuce, filin jirgin yana cikin duhu saboda rashin wutar lantarki. An horar da matuƙa jiragen da suke sauka a filin jirgin ta hanayar amfani da wutar lantarki ta dare.
Filin Jirgi Madeira:
Filin sauka da tashin jirage na Madeira yana ɗaya daga cikin filaye ƙalilan a duniya da injiniyoyi suka gina don su ƙara faɗaɗa shi.
Titin da jiragen ke sauka yana tsakayar teku ne. Lokacin da aka gudanar da aikin faɗaɗa aikin Titin jirgin, waɗanda suka tsara shi, sun lura da cewa mafita kawai ita ce a gina shi akan wani tsibiri da aka ƙirƙira. Wanda hakan yana haifar matsaninciyar wahala wajen sauka da tashin Jiragen.
Filin Jirgin MCAS Futenma, Okinawa:
Wannan filin jirgin yana daidai tashar mayaƙan sojin ruwa ne na ƙasar Amuka da ke Okinawa cikin ƙasar Japan. Hukumomin Soji na yankin sama da na ruwa, sun danganta wannan filin jirgin a matsayin wanda ya fi haɗari a duniya. Kuma filin jirgi ne da jirage masu ƙirar F/A-18Hornets da Ɓ-22 Osprey suke ci gaba da sauka a kansa.
Yankin ya fi yi wa jami’an Soja na ƙasar Amurka mahimmanci, wanda yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa suke amfani da shi wajen gudanar da ayyukansu.
Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa filin jirgin ke da haɗarin gaske shi ne, akwai ɗimbin gidajen jama’a a gefen filin jirgin, inda hakan kan haifar da ɗaukar matakin gaggawa akan wani yanayi.
Filin Jirgin Narsarsuaƙ A Greenland:
Daidai yake da filayen jiragen sama dake gefen teku kuma akwai sanyi sosai a wurin. Dusar ƙanƙara tana zagaye da shi kamar na tsawon kilo mita 1,800.
Titin da ke filin jirgin shi ne mafi haɗari a duniya. Sakamakon iri na yanayi, yana haifar da bugawar igiyar ruwa, wanda su ma matuƙan suna fuskantar matsala wajen tashi da saukar jiragensu. Bugu da ƙari, akwai matsala ta aman wuta da ke fita daga cikin manyan duwatsu, wanda hakan yakan shafi lafiyar injinan jiragen.