Filin Jirgin Saman Daukar Kaya Na Zamfara Zai Fara Aiki a 2021 – Matawalle

Daga Hussaini Yero, Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya bayyana cewa, a wannan shekarar ce filin jirgin sama na daukar kaya zai fara aiki a jihar.

Matawalle ya bayyana hakan ne ta bakin sakataren yada labaran gwamnarin jihar, Jamilu Birnin-Magaji a Gusau shekaean jiya Juma’a. Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne lokacin day a ziyarci wajen da ake yin wannan aikin da ke wajen garin Gusau.

Kwamishinan ayyuka na jihar Malam Ibrahim Mayana, ya yaba da yadda aikin ke gudana, musamman kan ingancin aikin. Sannan sai ya kara da cewa, za a gina wajen ajiye kaya da masaukin alhazai kusa da filin jirgin domin musamman ga Alhazai wadanda suka je aikin Gajji. Kwamishinan ayyukan ya ci gaba da cewa, da yardarm Allah za a kammala aikin tashar jirgi ba tare da an dade ba.

Exit mobile version