Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home NISHADI

FIM DIN GIDAN DAMBE A GIDAN DAMBE

by Muhammad
April 6, 2021
in NISHADI
3 min read
Dambe
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Maje El-Hajeej Hotoro,

Na riski mawaki Dauda Kahutu Rarara da ya shahara a wakokin siyasa a ofishinsa dake Zoo road a jihar Kano, mai mayar da umarni Iliyasu Abdulmuminu Tantiri ne ya jagoranci zaman. “Fim mai dogon zango nake son farawa, mai suna Gidan Dambe, kuma zan yi wannan fim ne domin taimakawa tsoffin ‘yan fim din Ibro, wadanda a yanzu an jingine su saboda kowa ya koma series. Ina so a rika ganinsu ko wasu za su daga a rika kiransu aiki. Kuma mutane da dama irinsu Adam Zango da Tantiri da Maishadda sun ce zaka iya, shi ya san a ce a kira ka, mu zauna mu tattauna ga tsohon dan wasan Ibro nan Bawa mai Kanwa yana da masaniya akan harkokin dambe sai a yi sharin idea”. A cewar Rarara.

Bayan kammala tattaunawa na koma ina tunanin ta yaya zan fara, tashin farko sai na hada marubutan da nake tunanin zasu taimakawa min a wannan aiki. A karon farko na tarihin rayuwata na kai ziyara babban gidan dambe na jihar Kano, domin samun karin haske. Na samu bayanai da yawa na rubuta labara kamar yadda na samu bayanai da yawa na karin ilimin rayuwa.

Harkar dambe a kasar Hausa na bukatar kwaskwarima da kuma kulawa, kamar yadda su kansu ‘yan damben ke matukar bukatar kulawa da kuma saiti. Siffofinsu sun koma siffar ban tsoro, saboda tsabar shan bugu, yayin da wasu da dama suka zama raunana wadanda a baya karfafa ne. ‘Yan dambe na rayuwa ne da shan kayan maye domin gusar da tsoro da samun kuzari, wanda hakan yana taka muhimmiyar rawa wajen raunata musu karfinsu a nan gaba. Kazalika yawancinsu na amfani da tsubbace-tsubbace da surkulle domin neman sa’a, maimakon mayar da hankali wajen motsa jiki. Baya ga haka babu wani kwakkwaran tanadi da ake yi dangane da lafiyarsu ko kuma gobensu.

Kamar yadda na fahimci ba mamaki da yawansu sun ta’allaka ne da wannan dambe ba tare da samun wata sana’a da zasu dogara da ita ba. Yawancinsu na dauke da askin banza a kansu wanda a al’adar Hausawa ana kallon masu wannan askin a matsayin masu karanci tarbiyya. Da yawansu suna da karancin ilimin addini da na zamani, kuma yawancinsu ba sa aure ballantana tunnain nan gaba idan karfinsu ya kare suna da masu tallafar rayuwarsu. Na fahimci hakan ne a gidan damben da aka gabatar da ajon wani dan dambe da yayi aure, inda mai gabatarwa yake kiran sunayen manyan ‘yan damben yana shawartarsu da su daure su rika aure a matsayin hanyar samar da zuri’a.

Wasu da yawa sun zama abin tausayi an ragargaza musu fuskoki da duka, ga karfi ya kare ga babu wata tabbatacciyar madogara, sannan ga shaye-shaye ya auri rayuwar su. Haka z aka gansu suna yawo cikin wani yanayi na abin tausayi wasu na roko ana dan taimaka musu da dan wani abu.

Wasan dambe na da dadin kallo ga masu ra’ayi, domin ana karbar Naira dari biyar (N500) a bakin kofar shiga kamar yadda a ciki ake karbar kudin kujerun zama a kalli wasa. Kamar yadda akwai masu bayar da kudi ga gwarzonsu lokacin da ya yi nasara, ko kuma yayi aure. Wani abu da na kasa ganewa shine cika da gidan ya ke yi da mata, musamman bisa la’akari da sanin cewa mata ba su fiya son abubuwan tashin hankali da firgici ba. Kuma a wajen ana iya fasawa wani baki ko hanci ko gefen ido. Duk da dai daga baya bincike ya tabbatar min da cewa manyan abokan ‘yan dambe sune Karuwai, Bokaye da kuma mahauta.

Wasan dambe hanya ce ta zama shahararre a duniya saboda yadda a yanzu kafofin yada labarai suka bas hi muhimmanci, sannan kuma kafar sadarwa na zamani na dauka su sanya shi ga masu sha’awar kallo a duniya. Gwamnati da ‘yan kasuwa suna sa gasar kudi da ababen hawa a matsayin gasa, wanda manyan ‘yan dambe daga ko ina suna zuwa ana kuma samun kudin shiga a wajen ‘yan kallo.

A wannan rubutu da muke yi muna kokarin nuna yadda gwamnati da ‘yan kasuwa zasu iya shiga harkar su kyautata was an dambe a matsayin was an gargajiya. Sannan mu shigar da illolin shaye-shaye da neman mata gami da zuwa wajen bokaye da rashin samun madogara a rayuwa. Sannan zamu yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin mawaki Rarara ya sa musu babbar gasa da zasu amfana a rayuwa, mu kuma jawo hankalin kamfanoni su gyara musu wajen damben wanda yana bukatar kwaskwarima.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

 Littafin ‘SAI YANZU’ Na Hanne Ado Abdullahi (1)

Next Post

An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

RelatedPosts

Kalubale Daya Tak Da Na Taba Fuskanta A Fagen Waka – Nura M. Inuwa

Kalubale Daya Tak Da Na Taba Fuskanta A Fagen Waka – Nura M. Inuwa

by Muhammad
1 year ago
0

Masu karatu da zarar an ambaci sunan Nura M. Inuwa...

Matasan Zamani                                                                              

Matasan Zamani                                                                              

by Muhammad
1 year ago
0

Gabatarwa Game Da Shafin Matasan Zamani   Tare da Sallama...

Shawara Kan Saka Turanci Cikin Wakar Hausa Hip Hop – Dabo Daprof

Shawara Kan Saka Turanci Cikin Wakar Hausa Hip Hop – Dabo Daprof

by Abdulaziz Kabir Muhammad
1 year ago
0

Daya daga cikin fitattun mawakan Hausa Hip Hop, Dabo Daprof,...

Next Post
An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

An Haifi Wani Yaro Da Azzakari Uku A Irak

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version