Fim Din ‘MATA DOZIN’ Ya Fito Da Matsalolin Da Mata Ke Fuskanta A Wannan Zamanin —Ibrahim Bala

Mata

A wannan hirar da LEADERSHI HAUSA ta yi da shahararren Jarumi, kuma marubuci, kuma mai Bada Umarni a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood mai suna IBRAHIM BALA wanda aka fi sani da Umar a cikin shirin Labarina, ya yi bayani game da sabon fim din da ya shirya, ya rubuta, ya kuma Bada Umarni, mai suna MATA DOZIN. Wanda a cewarsa fim din ya fito da sabon salo wajen fadakarwa gami da nishadantarwa don birge masu kallo da kayatarwa. Ya kuma yi bayani game da irin kalubalen da yake fuskanta wajen shirya wannan shiri, dama wasu batutuwan. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:

Da farko za ka fadawa masu karatu cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da sh

Sunana Ibrahim Bala wanda aka fi sani da Umar a cikin shirin Labarina.

Akwai wani sabon fim dinka me shirin fitowa mai suna MATA DOZIN na ga Jama’a na ta rubibi da tsumayen son ganin fitowar wannan fim, shin na ka ne ko kuwa bada umarni ka yi a ciki kamar yadda kake bayarwa a sauran fina-finai?

Kwarai fim din yanzu ake kan daukarsa shiri ne mai dogon zango wato ‘Series’, fim di na ne, nawa ne kuma ni ne na bada umarni.

Me fim din yake kunshe da shi, ganin yadda jama’a suke ta tsumayen fitowarsa?

Fim din na kunshe da matsaloli dake afkuwa cikin wannan zamanin musamman kan ‘Yan Mata, da yadda rayuwarsu ke kasancewa da samari da yadda ake samun  matsalolin zaman aure.

Me ya ja hankalinka har ka yi tunanin shirya fim a kan wannan matsalar?

Saboda sune matsalolin da ke damun al’umma yanzu ya zama wajibi matsayinmu na masu shirya fina-finai mu bada wata gudummawa da za ta taimaki al’umma kan abinda ya addabesu.

Kasancewar Jama’a na rubibin ganin shi wannan fim na ‘MATA DOZIN’, ya kake kara hango yanayin karbuwarsa a nan gaba ga su masu kallon bayan fitarsa, ganin yadda yake samun lambar yabo wajen mabiyansa duk da cewa a yanzu ake kan dora shi?

InshaAllah muna kyautata zaton karbuwarsa fiye da a yanzu musamman yadda ya zama irin shirin da mutane ke bukatar gani ne, hakan yasa muna sa ran zai karbu fiye da tunaninmu.

Ya batun rubutun fim din kai ka rubuta ko kuwa wani ne daban ya rubuta, kasancewar kaima daya ne daga cikin marubuta fina-finai?

Eh! kwarai kuwa ni na rubuta shi.

Ya ka ji lokacin da ka fara kokarin shirya shi wannan fim, ko akwai wani kalubale ko wata matsala da ka fuskanta game da shirya shi ko Bada Umarninsa?

Gaskiya ta kowanne  bangare na sha kalubale ya na yin rubutu da lokacin da nake warewa na rubutun, sannan wajen daukar aikin an samu matsaloli musamman akwai lokutan da zamu fito ruwan sama ya hana kuma ka riga ka dauko kayan aiki haya da saura abubuwan aiki, kuma akwai sababbin fuska cikin shirin to da dama wasu an sha artabo da su wajen daukar shirin MATA DOZIN.

Fim mai dogon zango za ka ga wani sa’in a lokacin da ake kan dora shi ko ake tsakiyar yinsa, wasu sai su yi kwadayin shiga cikin shirin, wanda kuma a baya ba mamaki an yi musu tayin shiga fim din, amma sai su hofuntar da abin sai daga baya su buka ci shiga, shin wannan fim na Mata Dozin kun samu irin hakan kuma an kayyade iya Jama’ar da za a yi da su har karshen fim din ko kuwa har yanzu kofa a bude take ga masu sha’awar shiga, me za ka ce akan hakan?

Gaskiya a farko ya samu da yawa sun ki shiga amma daga lokacin da aka fara daukar shirin Mata Dozin ya fara yawo sai akai ta yi min waya ana so a shiga saboda yadda aka ji shiri babba ne kuma ana sa ran in sha Allah zai daukaka yanzu ma akwai damar shiga a ‘season 2’ kofa a bude take.

Me za ka ce game da shi wannan fim din na Mata Dozin?

Gaskiya shiri ne da aka tsaya tsaf! ake daukarsa a nutse saboda lokaci zuwa lokaci ake daukarsa, saboda ya kwata ya kuma burge masu kallo. Shiri ne wanda idan ka fara kallonsa ba za ka so ya tsaya ba insha Allah, nan gaba kadan zamu saki tallansa da ranar da za a fara sakinsa duniya baki daya ta kalla.

Muna Godiya

Ni ma na gode.

 

Exit mobile version