Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya amsa tambayar da aka yi masa game da fara nuna fim din kasar Sin mai taken 731 a sassan kasar, inda ya ce, irin wannan fim na tunatar da jama’a muhimmancin koyon darussa daga tarihi, da kokarin wanzar da zaman lafiya.
Kakakin ya ce, Sin kasa ce dake bude kofa ga kasashe waje, kuma mai hakuri da tsaro. Ana maraba da jama’ar sassan kasa da kasa, ciki har da na Japan, su shigo kasar Sin don yin yawon bude ido, da karatu, da kasuwanci da kuma rayuwa. Haka kuma, Sin za ta ci gaba da tabbatar da tsaron baki ’yan kasashen waje dake zaune a sassanta. (Murtala Zhang)