Fina-finan Hausa – Zamani Riga! (6)

Dr. Ibrahim Shehu Liman Alkalami ibrahimshehu781@yahoo.com

Jama’a muna farin cikin sake saduwa a wannan shafi na alkalami, inda a muke waiwayar abubuwan da suka shafi halin da harkar fina-finan Hausa ke ciki a wannan zamani. A wannan mako zamu waiwayi matsayin al’umma ne masu kallon wadannan fina-finai. Wadansu na ganin cewa matsayin masu kallo shi ne kawai su sayi fina-finai su yi nishadi, inda ba su gamsu ba, sai su yi ta guna-guni da korafi a tsakaninsu. To haka abin ya dace da su, ko kuwa yaya abin ya kamata ya kasance?

Da farko dai bari mu taBo marubuta wasan kwaikwayo da na fina-finai da kuma ‘yan wasan da ke aiwatar da wadannan wasanni. A tattaunawar da muka yi a baya, mun bayyana cewa duka wadannan su ma daga cikin al’umma su ke, suna kuma kokari bayyana irin rayuwar da al’umma ke ciki ne, ko hango yadda zata kasance, tare da nuna wa al’umma dabaru da matakan kyautata zamantakewarsu ta hanyoyin nishadantarwa. To idan haka abin yake, su ma al’umma suna da alhakin nuna gamsuwa, ko kyamatar abin da aka rubuta ko nuna wanda ya yi hannun-riga da irin tsarin zamantakewarsu.

Duk da an ce ‘zamani – riga’, hakan ba yana nufin a kakaba wa ita al’umma wadansu halaye da suke gurBatattu ba ne, ko kuma mara sa amfani ba. Don haka alhakin su al’umma ne su san alfanu ko akasin haka da ke cikin irin wadannan fina-finai ko wasannin kwaikwayo. Haka kuma, dole ne masu kallon fina-finai su sami kafar bayyana ra’ayinsu da yin kokarin daidaita yadda fina-finan zasu dace da su yadda ba za a rika yin kitso da kwarkwata ba.

A ‘yan shekarun baya, na tattauna da masana kuma wadanda suka lakanci harkar  wasan kwaikwayo na Hausa, wato Alhaji Yuyusufu Ladan, da Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja) da kuma marigayi Alhaji Kasimu Yero dangane da abin da ya dace da masu kallo wasan kwaikwayo ko fina-fina-finai. Dukkansu bakunansu sun zama daya kan cewa lalli a tabbatar da cewa wasannin suna gamsar da muradun kyautata harshe, al’ada, dabi’u da gaba-dayan zamantakewar al’umma.

Misali, shi Alhaji Yusufu Ladan na da ra’ayin cewa lallai ne, kada ‘yan wasa su rika yin kazallaha su rika nuna abin da zai tozartar da kyawawan al’adu da tarbiyyar al’umma. Ita kuma al’umma wajibinta ne ta ankarar da cewa abu kaza da ake nunawa bai dace ba, yadda su ‘yan wasan zau gyara.

Shi kuwa Alhaji Usman Baba Pategi, yana cewa sau da yawa masu sauraron shirye-shiryensa na wasan kwaikwayo na Samanja da Duniya Budurwar Wawa, da suka hada da al’ummar gari da shugabanni irin jami’an Gwamnati da Sarakuna su kan bayyana masa ra’ayoyinsu kan abubuwan da suka dace. c irin wadannan tsokace-tsokace da suke yi musu na karfafa musu gwiwa da kuma ba su damar kyautata wasanninsu.

A nasa Bangare, marigayi Alhaji Kasimu Yero ya bayyana mini cewa, dole ne kowani wasan kwaikwayo kada ya zama ya saBa wa kyawawan al’adun al’umma, kuma kada a wuce gona-da-iri. Ya bayar da misalin yadda ya yi kokarin yin gyare-gyare a fim din Amina don ya dace da yadda aka bayyana al’ummomin da abin ya shafa, musamman Hausawa, Ibo da kuma Fulani. Danwasan kwaikwayon ya yi hannunka mai-sanda da cewa yin haka zai taimaka wajen samun karBuwar wannan fim a wajen al’ummomin da aka yi abin dominsu.

Daga bayanan da suka gabata, za a lura da cewa ita al’umma ta na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen kyautatuwa game da irin fina-finan da ake shiiryawa.

A ‘yan tsakanin nan, ana ta kace-na-ce dangane da yanayin fina-finan Hausa da ake samarwa, wasu na cewa suna samun gamsuwa da kumshiyar wadannan wasanni saboda suna samun nishadantarwar da suke nema.Wasu kuwa na ganin akwai sake, domin suna hangen wasu abubuwa da ke neman tozarta kyawawan al’adu da tarbiyya, musamman ma kunya da girmama na gaba. Ta iya yiwuwa ma, abubuwan da suka jawo yin kememe da al’ummar Jihar Kano, da ma wasu al’ummomi daga wasu wurare suka yi kan kokarin kafa Cibiyar shirya fina-finai da Gwamnati ta yi niyyar yi a Kano. Haka nan a ‘yan shekarun baya an kafa Hukumar da ta rika taka-burki ga kamfanoni da kungiyoyin masu shirya fina-finai a Kanon.

A nan za a iya famitar cewa su al’umma na iya bayyana matsayinsu domin kawo gyara, ba wai don hana fina-finai ba wadanda kowa ya yarda da cewa ana amfana da su, muddin sun tsare abubuwan da suka dace. Abin tambaya shi ne, to su al’ummar sun kuwa yi hoBBasa wajen bayar da gudunmuwar tasu?

Akwai shawarwari  domin ganin ana karBar shawarwarin al’umma dangane da fina-finan.

  1. Hukuma, wato Gwamnati a matsayinta na uwa-ma-ba-da mama, tana da alhakin samar da wata mahada da za a tara marubuta wasannin kwaikwayo da fina-finai, da ‘yan wasan kwaikwayo, da kamfanonin shirya fina-finai, da masana, da jami’an tsaro, da malaman addini, da shugabannin al’umma da sauran al’umma domin yin nazarin halin da harkar shiryawa da aiwatar da fina-finan suke, da kuma yadda ya dace su kasance.
  2. Kungiyoyin marubuta da shirya fina-finai su rika shirya taruka don saduwa da jama’a don jin ra’ayoyinsu da shawarwarinsu.
  3. Gidajen radiyo da talabijin su rika gabatar da shirye-shirye na musamman don jin ra’ayoyi da shawarwarin jama’a dangane da fina-finai da wasannin kwaikwayo.

Ida nana daukar irin wadannan matakai, lallai gudunmawar da al’umma za su rika bayarwa, za su taimaka walen daidaituwar harkar fina-finai na Hausa yadda ba za a sami saBani tsakaninsu da tsari da yanayin zamantakewar al’umma ba.

 

Mu kwana nan, sai a mako na gaba.

 

Exit mobile version