Finidi George Ya Fara Aiki A Matsayin Sabon Mai Horos Da 'Yan Wasan Super Eagles Ta Nijeriya
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Finidi George Ya Fara Aiki A Matsayin Sabon Mai Horos Da ‘Yan Wasan Super Eagles Ta Nijeriya

byRabilu Sanusi Bena
1 year ago
Finidi George

Ministan wasanni, John Enoh, ya kaddamar da tsohon dan wasan Nijeriya, Finidi George, a matsayin babban kociyan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles a ranar Litinin a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Sabon Kociyan Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, Finidi George, yayin da yake fara aiki a yau Litinin a Abuja
Sabon Kociyan Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, Finidi George, yayin da yake fara aiki a yau Litinin a Abuja

Sabon kocin na Super Eagles ya kuma zabi tsohon abokin wasansa na kasa, Daniel Amokachi da wasu ‘yan kasashen waje biyu a matsayin mataimakansa, Finidi ya bayyana hakan ne bayan bayyana shi ga manema labarai a hukumance a matsayin sabon koci a Abuja.

  • NFF Za Ta Gabatar Da Finidi George A Matsayinl Sabon Kocin Super Eagles A Yau Litinin
  • Kalubalen Da Ke Gaban Finidi George

Har ila yau ya kuma kuma bayyana Olatunji Baruwa a matsayin mai horar da masu tsaron ragar tawagar, Baruwa dai shi ne ya rike mukamin a karkashin tsohon kocin tawagar Jose Peseiro.

Tsohon dan wasan na Ajax mai shekaru 53, kuma tsohon kocin Enyimba Finidi ya ce babban burinsa shi ne ya lashe wasanni biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su kara da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin.

Ya yi kira ga kafafen yada labarai da su ba shi goyon baya, yana mai cewa aikin ba abu ne mai sauki ba, ina so na roke ku a matsayinku na kafafen yada labarai cewa muna bukatar goyon bayanku, don Allah.

Kafin yanzu Finidi ya kasance mataimaki ga Peseiro a gasar cin kofin Afrika na karshe da aka kammala a Ivory Coast, inda Nijeriya ta kare a matsayi na biyu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Next Post
Bangaren Samar Da Motoci Na Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba A Rubu’in Farko Na Bana

Bangaren Samar Da Motoci Na Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba A Rubu’in Farko Na Bana

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version