Firai Minista Abiy Ahmed na Ethiopia, ya nada mata rabin ministocin majalisar zartarwarsa, ciki har da ministar tsaro.
Da yake bayani kan matakin nasa ga ‘yan majalisar dokoki, Mista Abiy ya ce mata ba su faye “cin hanci da rashawa kamar maza ba” kuma za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A yanzu Ethiopia ce kadai kasar da take da wakilcin jinsi daidai a majalisar zartarwa a Afirka bayan Rwanda.
Haka kuma Mista Abiy ya rage yawan ministocin kasar daga 28 zuwa 20.
Tun bayan zamowarsa Firai Minista a watan Afrilu ya yi manyan sauye-sauye da dama.
Ya kawo karshen rikicin da aka shafe gomman shekaru ana yi tsakanin kasarsa da makwabciyarta Eritrea, ya kuma saki dubban fursunonin siyasa tare da saussauta matsin da ake fama da shi a fannin tattalin arzikin kasar.
Aisha Mohammed ce ta zama ministar tsaron Ethiopia ta farko.
‘Yar asalin yankin Afar ne da ke arewa maso gabashin kasar, ta kuma taba yin aiki a matsayin ministar gine-gine.
Muferiat Kamil wadda tsohuwar shugabar majalisar kasar ce ta zama ministar Zaman Lafiya.
Za ta dinga lura da al’amuran da suka shafi leken asirin kasar da tsaro da kuma hukumar ‘yan sandan tarayya.
Mista Abiy ya ce matakin sauye-sauyensa na bukatar ci gaba da magance matsalolin da suka jefa kasar cikin rudani.