Shugabar Makarantar Firamare ta ‘Yan Sanda da ke cikin karamar hukumar Funtuwa a jihar Katsina, Mrs. Beatrice Ogbe, ta bayyana cewa, makarantar firamaren da hukumar ‘yan sanda ta gina a garin na Funtuwa ta kowa da kowa ce, ba ta yaran ‘yan sanda ba ce kadai, wato ta al’umma ce bakidaya.
Shugabar ta bayyana haka ne a waja bikin yaye dalibai na bana a harabar makarantar da ke cikin karamar hukumar ta Funtuwa.
Mrs. Beatrice ta bayyana cewa, “yanzu haka Makarantar nada dalibai sama da dari biyu da talatin maza da mata kuma a cikin su ne muke bikin yaye dalibai talatin da hudu a wannan karon.muna godiya ga Allah akan wannan gagarimar nasara da muke samu a cikin wannan makaranta. Kuma mu na godiya da hazikan malamai da kungiyar Iyayan Yara, watau (PTA ) da kuma duk wadanda suka halarci wannan bikin yaye dalibai namu da fatan kowa ya koma gidansa lafiya amin.”
Babban bako mai jawabi, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda na Shiyar Funtuwa, Isah Garba ya bayyana farin cikinsa ganin yadda daliban suka taka rawar gain wajan Karatu da kuma Fareti kai kace ‘yan kwaleji ne, kuma yayi jinjina ga Hukumar makarantar da malamanta wajan cigaban makarantar.
Mataimakin Kwamishinan kuma ya dau alwashin ganin ciyar da makarantar gaba ta kuwane bangare dan ganin ta samu duk abunda ya kamata ta samu dan cigaba ta.
Shi ma a nasa jawabin Shugaban kungiyar Iyayan Yara na Makarantar, Alhaji Bishir Mai Kano ya mika godiyar sa ga Malaman makarantar dan ganin yadda daliban suka banbanta da sauran na makarantun da ke cikin funtuwa wajan karatu.
Alhaji Mai Kano ya kuma tabbatar da cewa’ kungiyar su zayi iyaka kokarinta na samur wa makarantar abunda ta ke bukata dan cigaban dalibai sunga