CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home DAGA BIRNIN SIN

Firaministan Australiya Ya Sa Kasarsa Ta Zama Abin Dariya

by CRI Hausa
December 2, 2020
in DAGA BIRNIN SIN
1 min read
Firaministan Australiya Ya Sa Kasarsa Ta Zama Abin Dariya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Kwanan baya, wani rahoton da ma’aikatar tsaron kasar Australiya ta fitar ya yi cikakken bayani kan yadda sojojin kasar suka aikata ta’asa, inda suka kashe fararen hula bayin Allah a kasar Afghanistan, ciki had da yadda suka yiwa wasu ’yan shekaru 14 maza guda 2 yanka rago, suka kuma jefa gawawwakinsu cikin kogi. Kasashen duniya sun yi tir da abubuwan da sojojin Australiya suka aikata a Afghanistan.

Duk da irin ta’asar da sojojin Australiya suka aikata a Afghanistan, firaministan kasar Scott Morrison bai nemi gafara daga wajen al’ummar Afghanistan ba, a maimakon haka, ya nuna rashin jin dadi da wani zanen da wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya wallafa a shafin Twitter, wanda ya yi tir da ta’asar sojojin Australiya. Mista Morrison ya bukaci kasar Sin ta nemi gafara daga wajen kasarsa. Ko da yake daga baya mista Morrison ya ce, to, shi ke nan, a sa aya a wannan lamarin, saboda an bukaci a gurfanar da wadanda suka kashe mutanen farar hula a Afghanistan a gaban kotu. Amma abin da ya yi ya nuna mana cewa, wasu wadanda suke kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam, suna nuna fuska 2 kan batun kare hakkin dan Adam. Suna yunkurin dauke hankalin jama’a, ba su so a bayyana hakikanin abubuwan da suka faru.
Idan shugabannin Australiya ba su kara kyautata halayyar sojojin kasar ba, ba su kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifi a gaban kotu ba, sannan ba su nemi gafara daga wajen jama’ar Afghanistan ba, sun ci gaba da damun kasar Sin bisa wasu hujjoji maras dalili, to, za su zubar da kimar kasar ta Australiya, da ma kasashen yammacin duniya gaba daya. (Tasallah Yuan)

samndaads

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yaushe Amurka Za Ta Daina Zargi Marasa Tushe Kan Kasar Sin?

Next Post

2023: ’Yan Majalisar Dokokin Kogi Sun Bukaci Gwamna Bello Ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa

RelatedPosts

Matasan Sin Da Afrika Sun Tattauna Da Nufin Inganta Kare Halittu

Matasan Sin Da Afrika Sun Tattauna Da Nufin Inganta Kare Halittu

by CRI Hausa
8 hours ago
0

Matasan Sin da Afrika, sun gudanar da wani taro ta...

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa

Alluran Rigakafin Kasar Sin Sun Sanya Kwarin Gwiwa Kan Yaki Da Annobar COVID-19 A Kasashe Da Yankuna Masu Yawa

by CRI Hausa
8 hours ago
0

Annobar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da yaduwa a...

Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin Na Taimakawa Kasashe Da Dama Yaki Da Cutar

Alluran Rigakafin Cutar COVID-19 Na Kasar Sin Na Taimakawa Kasashe Da Dama Yaki Da Cutar

by CRI Hausa
8 hours ago
0

A baya-bayan nan, wasu kasashe da yankuna sun amince da...

Next Post
’Yan Majalisar Dokokin Kogi

2023: ’Yan Majalisar Dokokin Kogi Sun Bukaci Gwamna Bello Ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version