Firaministan Kasar Bahrain Ya Rasu

Sheikh Khalifa bin Salman al Khalifa ya rasu yana da shekara 84 a duniya. Firaministan ya rasu ne da safiyar yau Laraba a asibitin Mayo Clinic dake Amurka, kamar yadda kamfanin dillancin labaru na kasar Bahrain ya ruwaito.

Sarkin kasar Sheikh Hamad bin Isa Al Khalifa, ya sanar da cewa za’a kwashe mako daya na zaman makoki a duk fadin kasar.

Exit mobile version