Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci babban taron mahawara na MDD karo na 80 a birnin New York na kasar Amurka, tsakanin ranakun 22 zuwa 26 ga watan Satumban nan.
A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, firaminista Li, zai kuma halarci wasu ayyuka da Sin za ta shirya, ciki har da taron manyan jami’ai dangane da shawarar bunkasa ci gaban duniya da Sin ta gabatar, kana zai gana da babban magatakardar MDD, da jagororin kasashe masu ruwa da tsaki kan batun. (Saminu Alhassan)