Abubakar Abba" />

FIRS Ta Kashe Naira Biliyan 300 Wajen Karbo Haraji A 2018

Hukumar tara harajin gwamnatin tarayya ta FIRS ta yi shelar cedar ta kashe naira biliyan 300.4 a cikin shekaru uku da suka shige daga shekarar 2016 zuwa shekararto 2018 wajen karbo haraji. Wannan adadin an samo shine a daga Hukumar a ranar Litinin data ganata a garin Abuja. Dokar data kafa Hukumar, ta bata damar cire kashi hudu na harajin data karbo a fannin Mai da kuma fannin da bai shafi man ba kafin tura sauran kudin a cikin asusun gwamnatin tarayya. Hukar ta FIRS mallakar gwamnatin tarayya ta na daya daga cikin hukumonin Dale tarawa gwamnatin haraji. Sauran Hukumonin sune, Hukumar kwastam da kamfanin NNPC. A bisa fashin bakin da aka yi ma naira biliyan 300.4 tsadar harajin da FIRS ta karbo, ya nuna cewar ya kai naira biliyan 85.99 da aka karbo a shekakarar 2016. Wannan ya kai kimani kashi 2.6 bisa dari na jimlar harajin na naira tiriliyan 3.30 da aka karbo a shekarar 2016. Na shekarar 2017 kuwa, Hukumar ta karbo naira biliyan100.3 na tsadar harajin daga cikin naira tiriliyan 4.02 da Hukumar ta FIRS ta karbo. A shekarar 2018 Hukumar ta karbo naira biliyan 114.1 India tsadar harajin da aka karbo ta kai naira tiriliyan 5.32 da aka tara a shekarar. Shugaban Hukumar na kasa Mista Babatunde Fowler ya ce, Hukumar ta na mayar da hankali wajen tarawa gwamnatin harajin ta hanyar karfafawa da kima yin hadaka da kamfanoni masu zaman kansu dana gwamnatin. Ya yi nuni da cewar, sakamakon halin da mai ya samu a kana a ciki, Hukumar ta sage tukuru wajen mayar da hankali don tarawa gwamnatin harajin, India tafiayar da hankali a fannin da bai shafi man fetur ba. Acewar sa, don ta comma burin hakan ta samar da shirye-shirye don tabbatar da kara tarawa gwamnatin harajin. A karshe ya ce, don comma burin tara. harajin, Hukumar ta FIRS ta wanzar da shiri na musamman don abi umarnin biyan harajin.

Exit mobile version