Hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana cewa, ta samu nasarar tattara harajin da ya kai na naira tiriliyan 4.178 a cikin watanni 10. Shugaban hukumar FIRS, Mista Muhammad Nami shi ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da rahoton harajin cikin gida da aka samu a wajen taron mahukunta haraji karo na 46, wanda ya gudana a garin Abuja. Nami ya bayyana cewa, an samu nasarar cimma kashi 99 na harajin da aka yi tsammanin samu a cikin watanni 10, wanda aka yi tsammanin samun harajin naira tiriliyan 4.230. Ya kara da cewa, a farkon wata ukun shekarar 2020, an amshi haraji daga daukacin jihohin kasar nan guda 36 ciki har da babban birnin tarayya na naira biliyan 974.197. a cewarsa, an samu karuwar kashi 1.39 idan aka kwatanta da wanda aka amsa a farkon wata ukun shekarar 2019 na naira biliyan 988.024.
“Tabbas cutar Korona ta rage samar da haraji musamman ma a wasu yankuna da ke cikin kasar nan wanda aka tattara harajin shekara a fadin jihohi 36, inda aka sami naira tiriliyan 1.334 a shekarar 2019.
“Mun dauki babban darasi a lokacin cutar Korona wanda ya janyo muka yi amfani da kimiyya da sauran dubaru wajen samun damar tattara harajin shekara a cikin kasar nan.
“Mu na da tabbacin samun goyan bayan masu ruwa da tsaki a bangaren haraji wajen cike gibin da ake samu a cikin haraji a cikin kasar nan,” in ji Nami.