Hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS) ta bayyana cewa, ta samu nasarar tattara jimillar harajin naira 4,952,243,711,728.37 a shekarar 2020. Ta dai samu nasarar cimma kashe 98 daga cikin naira tiriliyan 5.076 da gwamnatin tarayya ta yi tsammanin samu a shekarar. Shugaban hukumar FIRS, Mista Muhammad Nami shi ya bayyana hakan lokacin taron manema labarai wanda ya gudana a ofishinsa. A wajen wannan taro, Mista Nami ya bayyana cewa, duk da cutar Korona wacce ta illata tattalin arzikin Nijeriya da rage farashin danyan mai a kasuwan duniya da durkusar da harkokin kasuwanci da zanga-bangar EndSars wanda ya kawo cikas a wajen biyan haraji, amma bai hana hukumar FIRS samun tattara kudaden haraji mai matukar yawa ba fiye da wanda aka samu a shekarar 2019.
Da yake bayyana mahimman abubuwan ci gaba da hukumar ta samu a shekarar 2020, ya bayyana cewa, hukumar FIRS ta dauki matakai lokacin da farashin mai ya sauka kasa. domin haka, bangaren man fetur ne ke samar da sama da kashi 50 na haraji daga cikin ribar da ake samu na danyan mai a shekarun baya, amma a wannan karo kashi 30.6 kacal aka samu daga harajin a shekarar 2020. Haka kuma ya bayyana cewa, bangarori wanda ba na mai ba sun samar da harajin kashi 109 a shekarar 2020, wanda aka samu kashi tara daga cikin harajin shekarun baya. Mista Nami hukumar FIRS ta samu nasarar gudanar da gagaruwar haraji a shekarar 2020, sakamakon gajirciwar shugabannin hukumar. Ya ce, hukumar ta aiwatar da wasu canje-canje wadanda suka hada da gina kwazon ma’aikata da inganta yanayin jin dadin da walwalar ma’aikatar hukumar da samar da dubarun amsar haraji a kimiyance da kuma samun nasarar hadin kai da masu ruwa da tsaki da dai sauran su.
Mista Nami ya ce, “yana da matukar mahimmanci da masu biyan haraji da su yi kokarin ci gaba da biya, sanna ma’aikataan hukumar FIRS da ke fadin kasar nan da su ci gaba da aiki tukuru wajen amsar haraji kamar yadda suka yi a shekarar 2020.
“Hukumar FIRS tana tsammanin samun haraji a shekarar 201 fiye da wanda ta samu a shekarar 2020. Za mu ci gaba da gudanar da garambawul a cikin hukumar FIRS wanda ake sa samun nasara musamman ma a bangarori daban-daban na gudanar da amsar haraji. Haka kuma za mu ci gaba da inganta ayyukan bangaren mai domin samun gagaruman haraji a wannan bangare. Hakazalika, za mu gudanar da hadin da masu ruwa da tsaki domin samun nasarar inganta hanyoyin samun haraji mai yawan gaske a cikin kasar nan a shekarar 2021,” in ji shi.