Connect with us

ADABI

Fitacciyar Marubuciya Ummulkhair Kabir Aliyu Ta Kwanta Dama

Published

on

A ranar Alhamis ne da ta gabata 30/8/ 2018 ne fasihiyar marubuciyar ta kwanta dama. Rasuwar marubuciyar Ummulkhair Kabir Aliyu ta matukar girgiza marubuta, saboda shakuwarsu da ita da kuma halin kwarai da kyakkyawar mu’amala da marigayiyar Ummulkhair Kabir Aliyu take da shi. Marubuta da yawa sun yi ta rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta suna bayyana kyawawan halayenta da kuma dabi’unta, da kuma yi mata addu’ar fatan dacewa da Jannatul Firdausi.
Ummulkhair Kabir Aliyu ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci, ta rasu ta bar mijinta da kuma yara Biyu. Ummulkhair Kabir Aliyu, kafin rasuwarta ta wallafa littattafai guda Goma (10) marigayiya Ummulkhairi memba ce ta kungiyar marubuta ta Hausa Authors Forum da kuma kugiyar marubuta ta kasa reshen jahar Kano (ANA KANO) sannan ‘yar halaliyar kungiyar marubuta ce ta mata zalla wato Mace Mutum Writers Association.
Bayan fagen rubutun zube da aka fi sanin marigayiyar a kai, kuma gwana ce a fagen rubutun wakokin Hausa da kuma na yabon shugaban halitta (S.A.W.).

Takaitaccen Tarihin Marigayiya Ummulkhair Kabir Aliyu
Wace ce Ummulkhairi Kabir Aliyu?
An haifi Ummulkhairi a unguwar Mandawari/Marmara, cikin birnin Kano. Ta fara karatun Muhammadiyya, ta allo da ta dare, daga bisani aka saka ta a makarantar firamare ta Dandago Special Primary School Kano, a shekarar 1992. Bayan ta kammala, ta wuce zuwa makarantar yan mata ta GGSS shekara. Inda ta kammala a shekarar 2002. Bayan ta gama sakandare na, ya yi daidai da sauke Alkur’ani mai girma da ta yi. A cikin shekarar aka yi maya aure.
A cikin shekarar ne kuma ta samu gurbin karatu a School of Hygiene Kano yanzu haka tana da aure, da ‘ya’ya biyu. Sha’awarta ga karance-karance ya samo asali tun tana yarinya karama, amman hakan bai sa ta yi sha’awar rubutu ba.
Tunanin rubutu ya zo mata ne bayan ta samu wani labari daga makwabciyar ta. Labarin ya dugunzuma ta, tare da daga mata hankali, har ya tsaya mata a zuciya. Wanda har ya hana ta sukuni. A cikin wannan lokacin ne kanwarta ta bata shawarar wallafa littafi dan ganin yawan karance-karancen ta. Wadannan dalilai biyu da ta hada ne suka sa ta fara rubutu Labarin Mene Mafita, shi ne labarin da ya hana mata sukuni, har sai da ta rubuta shi, wandaya fito cikin shekarar 2007.

Jerin Sunayen Littattafanta:
1. Mene Ne Mafita?
2. Zumunci Ko So?
3. Duhu Da Haske
4. Mene Ne Laifin Zuciya?
5. Mijin Kaddara
6. Illar Furuci
7. Karkon Kifi
8. Biri Boko
9. Wani Hanzari
10. Tawakkali
Ta na fatan nan da shekaru da basu wuce biyar ba, mata su sami sauyin rayuwar su. Ya zamo ana damawa dasu ko ina kuma cikin kowace harka, musamman a fannin ilimi da wayewa tare da bunkusa sana’oi koda na hannu ne.
Ta ce mata su kara zage damtse gurin yin kafada da maza gurin neman ilimin addini dana zamani dana sana’a da ma duk wani ilimi indai sunan sa ilimi, ko ince karuwa. Dole sai mata mun fitar da lokaci da tsoro kafin mu cimma buri, amma tana yi mana wannan fatan duba da yadda mata suka dage gurin fita neman ilimi, bag manyan ba, kuma ba ga yaran ba.
Kuma mu dinga taimakan na kasa damu ko da da shawara ne, hakan zai kara mana zumunci da cigaban baki daya. Tana fatan nan da shekaru kadan muga mata na rike da manyan madafun gwamnati, haka a manyan makarantun koleji da jami’a, bare asibitoci da muke da karancinsu.
Amma duk hakan ba zai samu ba sai mun jajirce da neman ilimi don shi ne silar taka kowane matsayin rayuwa, Allah yasa mu kai gaci ameen.
Ummalkhairi ta rayu da marubuta cikin girmamawa da ladabi da biyayya, ba ta da abokin fada, tana da mutunci da kirki da girmamawa kowa. Allah ya ji kanta, ya gafarta mata.

(An ciro daga littafin Tarihin Mata Marubuta na Kilima Abba Abdulkadir)

Wakar Ta’aziyyar Marubuciya Ummulkhairi Kabir Aliyu Daga Nasiru G. Ahmad
Allahu akbar rayuwa,
Ba tabbacin dawwamuwa.

Ruhi aro ne anka ba,
Mu da lokacin kayyaduwa.

In lokacin ya hattama,
Dole mutum yai komuwa.

Ba don yana so haka ma,
Dukkansu dangi ‘yan uwa.

Tun safe naj ji habarin,
Rashi abin yin damuwa.

Na UmmuKhairi ‘yar uwa,
Mai kyan hali da nagartuwa.

Marubuciya kuma Sha’ira,
Fannin ga duk ta goguwa.

Matar kwarai mai kamuwa,
Kowa tana girmamuwa.

Hodarta kunya kowashe,
Kowa yana yin shaiduwa.

Na jimama da rashi nata,
Don ba ta halin kusuwa.

Ya katibai sai hakuri,
Haka sha’irai nai gaisuwa.

Allah ya kamsasa kabari,
Nata ya zam haskakuwa.

Ya Rabbana yafe mata,
Dukkan kure da ta zam yiwa.

Sanya makwancinta ya zam,
Raula ta zam ta ni’imtuwa.

Mu ma muna bisa gwadabe,
Kira naka mu yi amsuwa.

Allah idan loton ya zo,
Ka ba mu sa’ar komuwa.

Albarkacin Kur’anuka,
Da Rasulu bangon dafuwa.

Allah ya gafarta wa Ummulkhair ya haska makwancinta ya sa ta a
jannatul firdausi Ameen
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: