Tare da Sayyid Isma’il Umar (Mai Diwani)
Ranar takwas ga wata, wadda aka fi sani da ranar Tarwiyya (ranar cika salka da ruwa zuwa Minna a da, don lokacin babu ruwan fanfo a can. Babu Tanti mutum shi ne zai je ya kafa wa kansa bukka na zaman Mina, amma yanzu alhamdulillah Allah ya kawo ni’ima), Alhazan da suke Kirani ko Ifradi jira za su yi kawai rana ta fito su kama hanyar Mina.
Amma ga masu yin Tamattu’i, za su sake yin niyya da nufin Aikin Hajji tunda niyyar farko da suka yi ta Umura ce kawai, sai su fita zuwa Mina. Mai Hajjin Tamattu’i kamar yadda muka yi bayani a baya, daga nan masaukinsa na Makka (idan a nan yake) zai yi harama, ba sai ya je wani Mikati ba. Idan kuma a wajen Makka yake sai ya yi niyyar a Mikatin mutanen yankin da yake.
Ana so idan Alhaji ya kama hanyar zuwa Mina, ya rika yin addu’a da Talbiyya (Labbaikal Lahumma labbai…) har ya je Mina, a nan zai yi sallar Azuhur kasaru (raka’a biyu), La’asar kasaru, ya yi Magriba cikakkiya, Isha’i kasaru, sannan ya kwana.
Idan gari ya waye, ranar Arfa kenan, Alhaji ba zai fita zuwa Arfa ba sai bayan rana ta fito. Amma idan ya fita ma kafin rana ta fito, Hajjinsa bai baci ba sai dai bai yi koyi da Shugaban Halitta ba, Annabi (SAW).
Za a kama hanyar zuwa Arafa ana yin Kabbara, Hailala da Talbiyya (Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilaha illallah da Labbaikal lahumma labbaik…).
Muhammadu bin Abibakaris Sakafi (RA) ya ce, “Na tambayi Anas bin Malik (RA) a lokacin da ni da shi muke barin Mina zuwa Arfa cewa, yaya kuka yi da Annabi (SAW) da za ku bar Mina zuwa Arfa? Talbiyya kadai kuke yi ko dai akwai wani abu? Sai ya ce “A cikin mu akwai masu yin Talbiyya (babu wanda ya ce musu komai), a cikin mu akwai masu yin Kabbara, akwai kuma masu yin Hailala (duk babu wanda ya ce musu komai).” Bukhari ya ruwaito Hadisin.
Wannan ya nuna kowanne za a iya yi, idan ma mutum ya hada zai samu dukkan falalar.
An so a sauka a Namira, wurin da Masallacin Arfa yake, a yi wanka (irin na janaba) da niyyar wankan tsayuwar Arfa. Amma fa ba dole ba ne yin wankan.
An so Alhaji kar ya shiga filin Arfa sai bayan rana ta yi zawali (ta gota tsakiya, ma’ana lokacin Sallar Azuhur). Amma yanzu tunda hukuma ce take tafiyar da abin, babu laifi a tafi kafin lokacin, saboda yawan al’ummar kasashe da ake jigilar zuwa da su Arfa din ma, kafin a kai kowa masaukinsa na wurin, ranar ta yi zawali.
Za mu dakata a nan, idan Allah ya kai mu mako mai zuwa za mu dora da bayani a kan Tsayuwar Arfa da falalarta, Albarkar Annabi (SAW).