Fadar shigaban kasa ta bayyana cewa, Nijeriya ta fita ne daga cikin matsin tattalin arziki sakamakon shirin da gwamnatin tarayya ta aiwatar na farfado da tattalin arziki. Mashawarcin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya bayyana hakan wanda ya kara nuna cewa, ‘yan Nijeriya su kara shirin aiwkatar da wasu sababbin shirin wadanda za su karfafa tattalin arziki a cikin kasar nan. Mista Akande ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai kan nasarar da aka samu na aiwatar da shin farfado da tattalin arziki wanda ya kara yawan kudaden shiga a tsakiyar shekarar 2020.
Shugaban kasa da majalisar zantarwa ne suka amince da kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki tun a watan Yuni wanda mataimakin shugaban kasa yake jagorantar shirin. Nijeriya ta fita daga cikin matsin tattalin arzikin da ta shiga a tsakiyar shekarar 2020, inda ta samu karuwar kashi 0.11 daga cikin kudaden shiganta.
Mista Akande ya bayyana cewa, tun daga wata ukun shekarar 2020, aka fara shirin farfado da tattalin arzikin Nijeriya.
“Kamar yadda muka bayyana a shekarar da ta gabata bayan kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki kamar yadda gwamnatin shugaban kasa Buhari ya shelanta a kan tattalin arzikin Nijeriya.‘Yan Nijeriya su shirya kara samun wasu shirye-shiryen tattalin arziki daga wannan gwamnatin,” in ji Mista Akande.
A cewar Mista Akande, an samu karuwar kashi 0.11 daga kudaden shiga a cikin wata hudun shekarar 2020, bayan da Nijeriya ta shiga matsin tattalin arziki sakamakon cutar Koron wacce ta haddasa.
“An samu karuwar kashi kudaden shiga a wata hudun shekarar 2020, daga matsin tattalin arziki da aka samu a gaba daya shekarar 2020.
“Rahoton bayanan kudaden shiya yana da matukar mahimmanci bisa dalilai masu yawa. yana nuna mahimmancin karuwar bangaren sauran fannoni wadanda ba na mai ba, an samu karuwar kashi 92.68 a wata hudun shekarar 2020. Fannin da ya fi bunkada wanda ba na mai ba shi ne, bangaren fasahar sadarwa wanda ya samu bunkasa a lokacin cutar Korona.
“Haka kuma sauran fannoni da suka samu bunkasa wadanda ba na mai ba sun hada da bangaran harkokin noma da masana’antu da hakar ma’adanai da gine-gine.
“Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa, ta bibiye bangaren mai wanda aka samu kashi 19.76 a wata hudun shekarar 2020 fiye da wanda aka samu a wata hudun na shekarar 2019 a bangaren mai. Ana hako gangan daanyan mai miliyan 1.5 a kowacce tana, an samu haka ne sakamakon umurnin da kungiyar kasashe masu tattalin arzikin mai suka bai wa Nijeriya,” in ji shi.
Gwamnatin tarayya ta samar da shirin farfado da tattalin arziki ne sakamakon irin durkushewar da cutar Korona ta yi wa fannomin tattalin arziki a Nijeriya tare da samun bunkasa bangarori wadanda ba na mai ba a cikin kasar nan.
Mista Akande ya ci gaba da bayyana cewa, tattalin arzikin Nijeriya yana ci gaba da bunkasa kamar yadda asusun bayar da lamuni ta duniya da bankin duniya suka yi hasashe. Ya kara da cewa, tattalin arzikin Nijeriya ya karu ne duk da matsaloli wadanda suka hada da farkon dokar hana zirga-zirga da hargitsewar harkokok kasuwanci da matsalolin farashin mai wacce cutar Korona ta haddasa a kasuwan diniya da dai sauransu.