Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home AL'AJABI

Fitattun Kungiyoyin Asirin Da Ake Tsoro A Duniya

by Tayo Adelaja
September 27, 2017
in AL'AJABI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abubakar Abba

Wadannan kungiyoyin asirin, sun yi kaurin suna wajen aikata nau’ukan asirai a duniya, kuma sakamakon ayyukan nasu na asiri har sun kai matsayin suna kawo  rudu a duniya, musamman ganin abubuwan shu’umanci da suke aikata wa.

samndaads

Babbar tambaya anan itace, shin da farko ma, me yasa ‘ya’yan irin wadannan kungiyoyin suka rungumi dabi’ar ta asiri?

Ire-iren wadannan kungiyoyin, tuni sun yi nisa wajen canzawa wasu mutane dabi’unsu. har da yin kutse a harkar gwamnati.

Wadan nan manyan dalilai guda biyu na wadannan kungiyoyin asirin, ya sanya dole al’ummar suke jurewa da irin wadannan dabi’u da duk wani nau’in asiri da suka cusa masu.

Koda yake, wasu daga cikin ayyuka da kungiyoyin suke aikatawa, na wasun su yafi ban tsoro.

Wannan sharhin zai  a zayyana fitattun kungiyoyin asiri da suka yi fice a duniya wajen aikata asiri.

 

Kungiyar Gungu 36

Wadannan kuniyar ta asiri ba wanda aka saba dasu bane, domin kuwa sun fi kama ne da gaggan gungun ‘yan asiri, duka cewar su ma sun shiga cikin sahun sauran kungiyoyin asirin.

Kungiyar a kasar Malesiya take kuma itace tafi ban tsaro a cikin jerin kungiyoyin na asiri fitattu a duniya kuma yau a kasar, akwai dimbin ire-iren wadannan gungun na kungiyar asirin.

Kungiyar tana yin iya yinta, wajen bai wa ‘ya’yanta kariya, su na kuma zabar shugaban ta hanyar gudanar da zabe.

‘Ya’yan kungiyar sun  hada da kabilar kasar Chana maza kuma mafi yawancin ‘ya’yanta, sun yi kaurin suna wajen aikata ta’addanci.

Ayyukan ta nata kara bazuwa a duniyada kuma ta shafe shekaru da dama tana aikata ta’addanci, inda sai kara faskara take sakamakon karkarfan ginshiki da jigojinta sukayi mata tun lokacin da suka kafata.

Yawancin ‘ya’yanta ‘yan gurguzu ne, kuma akwai ‘yan kabilar kasar Chana  wadanda suke taka rawar zuba jari, inda ma su gwagwarmaya suka yi suka akan hakan.

Kudaden da suke zubawa akan kungiyar, don ‘ya’yanta su ci gaba da cin Karen su ba babbaka, su na samun kazamar riba akan aikata tasar da kungiyar ke gudanar wa.

 

Kungiyar  Zinare Mai Zagaya

Wannan kungiyar  mafi yawancin ‘ya’yanta, Bayi ne da aka haura dasu daga nahiyoyin Kasashen   Afirka zuwa nahiyar Turai kuma sune na farko da aka fara kirkirowa a tsakiyar  karni na 19. Sun dade da yin karfi, asalinsu suna zaune a Arewacin kasar Amurka tun lokacin yakin

cikin gida na kasar.

Dakta George W. L. Bickley ne ya fara bude mata reshe na farko a garin Cincinnati a cikin shekarar 1854.

A hankali ta koma zuwa Kudanci, inda aka amshe ta hannu bi-biyu. Tun da farko manufar ta shine, kafa rundunar da zata mamaye Arewacin kasar Meziko a bisa kudirin kara habaka kasuwanci Bayi, sai dai kuma sakamakon yakin cikin gidan, a kasar, ta maida hankalin ta wajen goya wa Kudu baya.

Wanan kungiyar ta asiri, ita ce ta Kwaleji tilo a kasar wadda matasa ‘ya’yan ta, basu cika jin tsoron ta ba.

Cike take da kulle-kulle na munafurci wajen gudanar da ayyukan ta, an kuma dora laifi akan ta na cewar ta hanyar ta aka kashe Tsohon Shugaban Kasar Amurka John Kennedy, da kuma zargin kirkiro da Bam na kare dangi.

Saboda da karfi da kungiyar keda shi, ya jefa tsoro a cikin alumma, inda har ake rade-radin cewar itace ta rikide ta koma sananniyar kungiyar asiri dake fadin duniya.

‘Ya’yan kunhgiyar sun hada da zuri’ar  Rockefeller da Tsohon Shugaban Kasar Amurka  George W. Bush.

Ana kuma zargi kungiyar ce ta tone Akwatin Gawar gwarzon mayaki na yankin Apache mai suna Geronimo suka kuma sace kokon kansa da kasusuwan sa biyu suka kuma baje kolin su a shalkwatar su.

 

Kungiyar Firimason

Tana daya daga cikin tsofaffin kungiyoyin asiri a duniya. Misali na farko da ake gane kungiyar ta sabon ya yi, an kafa ta ne, a shekarar 1717 a kasar Ingila, shedar irin wanannan kungiyar itace ta  Masonic da a har yau take bada mamaki akan ayyukan ta na gudanar da asiri.

Yaren da alamomi da ake amfani dasu wajen aikta asiri, sun yi kama da na tsawon karni na kusa-kusa, sannan kuma su na amfani da hanyar rubuce-rubucen da suka yi suka aje tun a tsakiyar karni na shekarar 1300.

Kungiyar tana bada mahimmanci akan ‘yancin mutane na inganta rayuwar su, sai dai kungiyar ta yi kakkausar suka akan imanin da mabiya addinin Kirista suka yi.

Saboda tsagwaron bada kai wajen bauta tare da hujjoji da dama, har ta sanya dimbin ‘ya’yanta ma su karfin gaske, kamar Mozart da kuma yawan shugabanin kasar Amurka a cikin ta ya jefa tsoro a zukatan mutane, inda ake ganin sun samo karfin ikon sune, saboda kasancewar su ‘ya’yan

kungiyar.

Kungiyar tana yin iya kokarin ta wajen bai wa ‘ya’yanta kariya har zuwa iya tsawon rayuwar su da kuma hukunta makiyan su.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Tasirin Al-makura Ba Zai Gushe Ba a Nasarawa

Next Post

Hattara Dai Inyamurai! (I)

RelatedPosts

Abba Kyari Nawa!

Abba Kyari Nawa!

by Sulaiman Ibrahim
9 months ago
0

Abokina ne da dukkanin ma’anar aboki, majibin lamurrana da dukkanin...

Hello world

by Leadership Group
2 years ago
0

Amfani Ruman Ga Lafiyar Dan’adam

by Sulaiman Ibrahim
2 years ago
0

Shi dai itacen ruman a turance ana kiran sa da...

Next Post

Hattara Dai Inyamurai! (I)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version