Masu iya magana suka ce ‘komai ya yi farko zai yi karshe’. Tabbas wannan batu kam haka yake, idan muka yi duba da cewa, kamar yau ne ranar wata Laraba da ta gabata makonni akalla 50 da suka wuce, wato ranar 1 ga Janiru, 2020 ta zama ranar murnar sabuwar shekarar 2020 ga daukacin al’ummar duniya, wacce a yau tuni muka yi bankwana da ita a ranar wata Alhamis 31 ga Disamba, 2020, da ta zama ita ce ranar karshe a cikin shekarar ta 2020. Shi ke nan ta wuce sai dai tarihi ya dingi tunawa da ita, saboda tarin abubuwan da suka faru a cikinta masu dadi da akasin haka har ma da na alhini.
Cikin tunawa da abubuwan da suka faru a cikin shekarar ne, wannan fili namu na ADABI A YAU zai yi waiwaye a cikin shekarar ta 2020, ya tato mana irin tarin littattafan hikayar da aka samar a cikin shekarar, kuma ya yi mana tsokaci a kan wasunsu da su ne suka zama mafi shahara a cikin shekarar da kuma dalilan da ya sa suka yi tashe fiye da takwarorinsu.
Duk da cewar shekarar ta 2020 ta zo da wani irin yanayi a kasuwar adabin Hausa, saboda karancin samuwar sababbin littattafan hikayar fiye da shekarun baya. Wanda ba komai ya kawo hakan ba face tabarbarewar tattalin arziki da ya nakasa kasuwar adabin. Saboda me? Saboda makarantan kowa ta kansa yake yi, hankalinsu ya karkata ga abincin da za su ci su rayu, ba wai ta abubuwan nishadi suke yi ba, saboda yunwa da bakin talauci da ya yi wa ‘yan kasa kaka-gida. A gefe guda kuma ga dan karen tsada da kayan aikin dab’i suke yi, wanda hakan ya sa farashin littafi ya yi tashin gwauron zabi fiye da yadda aka saba da shi.
To amma me? Duk wannan ba ta hana wasu marubutan wallafa littattafansu ba. Haka wasu makarantan ma ba su fasa sintirin zuwa kasuwa neman littattafan karantawa ba. Domin dama masu iya magana sun ce: ‘Inda wani ya tsaya, to daga nan wani yake farawa.’ Haka marigayi Garba Supa yake fada a cikin wakarsa yake cewa:
Ana fadi ana babu kudi gari,
To duk wanda yake fadi shi ne bai da shi.’
Lallai wannan batu na marigayin haka yake, domin duk da tabarbarewar tattalin arziki da mawuyacin halin da kasar take ciki, za mu ga cewa wasun mu na gasar gina manyan gidaje, da hawa zunduma-zunduman motoci, da fita yawon shan iska daular larabawa ko kasashen turai. Hatta ga ‘ya’yan talakawan da iyayensu ba su da cin yau balle na gobe na gasar rike tamfatsa-tamfatsan wayoyi da dinka manyan shaddodi.
Kai! Kar dai mu nausa daji. Bari mu koma kan batunmu, na alkawarin da muka yi na kawowa masu biye da mu a cikin wannan fili fitattun littattafan hikaya a shekarar 2020 da ta gabata.
Aalimah: Littafin ‘Aalimah’ ma iya cewa shi ne littafin da ya zama gagara-badau a shekarar ta 2020 saboda yawan masiya da yabo da littafin ya sha. Marubuciya Sumayya Abdulkadir (Takori Kabara) ita ce ta rubuta littafin na ‘Aalimah’. Ba Aalimah kawai ba, kusan duk littattafanta sun yi amo a cikin shekarar ta 2020, fiye da na kafatanin marubuta littattafan hikaya. Ta ciri wannan tutar ne da littafin nata dake amsa sunan ‘Aalimah’ wanda ta yi shi daga na Daya har zuwa na Hudu. Bayan ‘Aalimah’ marubuciya Sumayya Abdulkadir Takori ta dawo da wasu tsofaffin littattafanta na baya, wadanda babu su a kasuwa ta sake wallafa su, amma cikin hukuncin Ubangiji sai ga shi an ci kasuwarsu fiye ma da wasu sababbin littattafan. Sai dai mun ambaci ‘Aalimah’ ne kadai saboda shi ne littafin da aka fara wallafawa a shekarar ta 2020.
Kwasar Ganima: FItacciyar marubuciyar littattafan hikaya da fina-finan Hausa, wato Fauziyya D. Sulaiman ita ce ta rubuta littafin na ‘Kwasar Ganima’ kuma aka wallafa shi a cikin shekarar ta 2020. Littafin da ya zo da sabon salo a cikin rubuce-rubucen marubuciyar. Saboda ‘Kwasar Ganima’ littafi ne guda Daya tilo da kuma ya kunshi gajerun labarai har guda Ashirin Da Biyar, wanda irinsa suka yi karanci a kasuwar adabi. Bugu da kari kuma littafin ya samu ingancin bugu. Domin ni dai a kaf kasuwar adabi ban ga littafin da ya samu ingancin bugu kamar sa ba a cikin shekarar ta 2020.
Ni Ma ‘Ya Ce: Littafin ‘Ni Ma ‘Ya Ce’ sabuwar marubuciya mai sa’a Zainab Abubakar Kaugama ce ta rubuta shi. Shi ne littafinta na Biyu da ta wallafa, na farkon dai shi ne GARKUWATA. Dadin da littafin ‘Garkuwata’ ya yi wa makaranta, shi ne ya sa da ta fito da ‘Ni Ma ‘Ya Ce’ aka yi rububin sa. Kuma cikin yardar Allah shi ma ya zamu karbuwa a gurin makaranta fiye ma da ‘Garkuwata’ din.
Gwarzon Sadauki: Fasihin marubucin littafin yaki da sunansa ya karade kasar Hausa, kuma aka sallama masa a fagen rubutun littafin yaki, wanda ake yi wa kirari da ‘Sarkin Marubutan Yaki’ wato Abdul’Aziz Sani Madakin Gini. Shi ne ya rubuta littafin na ‘Gwarzon Sadauki’. Littafin da shi kadai ne kwal littafin yaki da aka wallafa a kaf cikin shekarar ta 2020. Ashe ke nan dole littafin ‘Gwarzon Sadauki’ ya yi sharafi a fagen littattafan yaki saboda kasancewar sa tsoka Daya a miya saboda ba shi da kishiya.
To bayan wadannan littattafai akwai wasu da dama da suka yi tashe a cikin shekarar ta 2020, kamar su:
Wukar Fawa – Hassana A. Hunkuyi
Daukar Fansa – Aisha Asas
Rubutacciya – Fatima Garba Danbarno
Kishin Mijina – Asma’u M. Gombe
Matar Sarki – Hadiza Bara’u G/Iko
Zamanin Ke nan – Ummi Ma’aji
Ummu Adiyya – Azizah Idris Gombe
‘Yancina Ne – Humaira Lawan Zango
Tuhuma – Amina Jibrin