Connect with us

Madubin Rayuwa

Fitattun Mata: Barista Rabi Waya Ko-kun-san?

Published

on

Barista Rabi Waya mace mai kamar maza, ita ce Sakatariyar bayar da shawara wa hukumar amsar korafe-korafen jama’a ta jihar Kano, gabanin nan, masaniya a harkar shari’a ta yi aiyuka da dama a wurare daban-daban wanda hakan ya sanya ta goge sosai a aikin ‘Lauya’. Barista ta sha samun lambar yabo a bisa hazakarta, domin hatta magabatanta a aikin Lauya sun sha daga mata hanu su sara mata sakamakon yadda take shiga kotu ta kare masu gaskiya har ta samu nasara a shari’u da dama, har-ila-yau tana daga cikin masu yaki da cin zarafin mata da kuma keta musu haddi.

Wace ce Barista Rabi Waya?

An haifi Barista Rabi Waya ne a ranar 2 ga watan Disamban shekara ta 1971. Ta fara karatun Firamare  a makarantar Masallaci furamare a 1975, sannan a lokacin tana makarantar Islamiyya ta Yolawa tana aji 4 sai aka mayar da ita  furamaren je-ka ka-dawo ta Gidan Galadima ta ’yan mata. Sai ta tafi sakandarin WATC, Goron Dutse, a shekarar 1981. Bayan ta kammala sai ta tafi kwalejin nazarin ilimin addini da shari’a da ke Aminu Kano ‘College of Islamic Studies’ wato Legal, da farawarta ne kuma sai ta yi aure ta jingine shi karatun a wancan lokacin. A shekarar 1988 ta fara koyarwa a makarantar furamaren Madatai tsawon wata shida. A shekarar sai ta sami gurbin shiga jami’ar Bayaro inda ta yi diploma a Hausa-Arabic da Islamic studies, ta gama a 1992. Daga nan sai ta yi sha’awar sauya kwas. Tun lokacin da take ‘legal’ tana da sha’awar zama lauya. Cikin ludufin Allah a shekara ta 1992 ta sami gurbin karantar lauya a jami’ar Bayero da ke Kano, inda ta karanta ‘Shari’a and cibil law’  ta kammala a 1998, sai kuma ta hanzarta zuwa ga yi wa kasa bauta, dawowarta ke da wuya sai ta sake halarta kwas din da zai sanya a kira ta da suna ‘LAUYA’ a tsakanin 1999-2000.

Aiyukan Barista Waya:

Lauyar mai kamar maza (kodayake a aikin shari’a babu mace babu na miji dukaninsu maza ne) bayan kasancewarta cikakkiyar Lauya, ta fara aiki da Chambar S.H Garun Gabas and Co. Daga nan kuma lifafa ta cilla a 2001 kuma ta samu aiki da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, a shekarar 2003 aka mayar da ita hukumar bayar da ilimin bai-daya ta jihar Kano (SUBEB)  a matsayin mai bayar da shawara kan shari’a. Ta yi ta wannan aikin daga 2003 zuwa 2007,  har-ila-yau aiki ya sake kai ta ofishin amsar korafe-korafen jama’a da kuma yaki da rashawa wato ‘Kano State Public Complains and Anti-Corruption  Commission a 2015 wanda kuma a halin yanzu Barista take a matsayin Sakatariyar bayar da shawara kan hidimar da ta jibinci shari’a.         Kafin aikin gwamnati Hajiya Rabi tana taba sana’o’i na cikin gida, wannan ta sa ko bayan zamontowarta babbar lauya ba ta daina sana’a ta saye da sayarwa ba irin na mata, kuma tun da fari ma mun shaida muku cewar ta taba aikin koyarwa.

Kasantuwarta mace mai kishin Hausa-Fulani, ta tsunduma kanta cikin fannoni daban-daban domin taimaka wa jama’a musamman wadanda ake zalumta ko aka zalumta, mace ce mai kwazo wanda hakan ya sanya abokan aikinta da ogoginta suke sallama mata dari bisa dari a bisa yadda take zagewa ta yi aikin Lauya daidai da kowani namiji, takan shiga kotu ta kasa ta tsare ta sha yin nasara a shari’u da dama.

Filin fitattun mata ya tambayi Rabi Waya kan yanayin aikin Lauya ga mace ta amsa mana da cewa, “Gaskiya aikin Lauya aiki ne mai muhimmanci ga mace, kuma yana da gayar wuya, domin aiki ne wanda za ka kare hakkin jama’a musamman mu lauyoyin gwamnati aiki ne a kanmu kare mutuncin jama’a da gwamnati. Aiki ne da ba a duniya kadai yake da tasiri ba har a lahira yadda za ka tsaya ka mayar a gaban Ubangiji dole sai kana taka-tsan-tsan da kare gaskiya da fadin gaskiya.

“Kullum muna tuna mu Hausawa ne Musulmi kuma mata to aikin yana zuwa mana da sauki. Sannan a fagen amana ba yabon kai ba mata suna da wannan kokarin shi ya sa da wuya ki gan su a irin rigingimu musamman lauyoyin gwamnati. Amma a rayuwar da muke ciki mata akwai bukatar su fito su kara jajircewa ko don ‘yan’uwansu mata. Bahaushe na cewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne don haka matsalolin da ke addabar mata a yau na zalunci da fyade musamman a wannan rayuwar sai mata sun fito su tsaya don kare martabar ‘yan’uwansu mata. Za a kawo yarinya karama shekara uku zuwa sama an yi mata fyade mata mu ke da alhakin kula wannan cin mutuncin matan da ake yi,”

Ta kara bayani wa filin nan da cewa “Mata su suke dauke da kalubalen rayuwa idan miji ne ya lalace mace ce idan Da ne ya lalace mace ce dai Allah ya sa tarbiyya hannun mace don haka mace, amma an bar mata ana take hakkinsu da shari’a da addini ya ba su hatta wasu hakkokin al’adarmu ta ba mu amma don zalinci sai a danne wanda mace ita ta fi dacewa da ta taimaka a kwato wannan hakkin”.

Barista Rabi ta yi nuni da cewar shigowar mata harkar shari’a wata dama ce ta kawo ci gaba wa al’umma, tana mai kokarin fadakar da mata ‘yan’uwanta a kowane lokaci domin ganin mata suna shigowa ana damawa da su, tana mai imanin cewa mata su ne suke da hakkin sauraron matsalolin ‘yan’uwansu mata. ‘Wata za a zalumce ta amma idan lauya namiji na tambayar ta ko ta ji kunya ta ki fada masa komai ko kuma dai wani abu, amma in mu mata ne za ta shaida mana komai’.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: