FITATTUN MATA: Sarauniyar Kyau Grace Oyelude

Madam Grace ita ce sarauniyar kyau ta farko a Nijeriya a gasar da aka yi 1957?

An fara gudanar da gasar kyakkyawar mace ko kuma sarauniyar kyau a Nijeriya ne tun a shekarar 1957. Malaman tarihi sun bayyana cewa alkalan gasar lokacin sun fara ne da zaben ‘yan takara ta hanyar hotuna a matakin share fage. Idan mace ta yi nasara a matakin, sai su gayyace ta, ta halarci gasar a mataki na karshe.

Tsarin gasar a wancan lokacin ya fi mayar da hankali ne kan bayar da tarbiyyar mata, sabanin yadda ya sha bamban da na yanzu. Na farko, ba a nunar da tsiraici kamar yadda yanzu a ke yi. A lokacin da ta shiga gasar, Madam Oyelude tana aiki ne a kamfanin United African Company (UAC), amma saboda sha’awar gasar ta wakilci Arewa, kuma ta samu nasarar kasancewar mace ta farko a Nijeriya, wadda ta fara taka wannan matsayi.

Jim kadan bayan nasarar da ta yi, Sarauniyar ta ziyarci kasar Ingila, inda ta yi amfani da damar da ta samu wajen shiga makarantar koyon aikin likita akwalejin Ashford Kent da ke birnin Landan.

Bayan nasarar da ta samu a kwalejin, Oyelude ta ci gaba inda ta kara karatu mai zurfi a fannin likitanci a shekarar 1962. Har ila yau, a kasar ta Ingila ta shiga kwalejin Royal College of Nursing, inda ta samu karamin Difiloma da babbar Difiloma a shekarar 1976. Madam Atinuke ba ta yi kasa a gwiwa ba ta halarci wata babban kwaleji a kasar Ghana, inda a nan ma ta zurfafa karatu fannin tsangayar nazarin gudanarwa da sha’anin mulki.

A yayin karatunta a kasar Ingila, Oyelude ta yi ayyuka da dama a asibitoci manya da kanana. Bayan ta dawo gida, Sarauniyar ta yi aiki a babban asibitin Kaduna, wanda a yanzu a ke kira asibitin Barau Dikko, tsakanin shekarar 1964 zuwa 1965.

Sarauniyar kyan ta yi ayyuka da dama a fannin kiwon lafiya. Daga Kaduna, an yi mata canjin aiki zuwa Makurdi a lokacin da yakin basasa ya barke a kasar nan, cikin 1967, inda nan ma ta rika bayar da gagarumar gudunmawa  wajen bayar da taimakon farko ga wadanda sanadiyyar yaki suka jikkata.

An haifi Sarauniyar kyan a Nijeriya a ranar 16 ga Nuwamba, 1931. Mahaifinta, James Adeleye Olude dan gidan sarautar Isanlu ne a Jihar Kogi, amma a Kano ta tashi cikin Hausawa, inda ta yi karatun firamare da sakandare tsakanin shekarar 1940 da 1952 a birnin Kano. Madam Grace na daya daga cikin fitattun matan Nijeriya, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen rayawa da habaka harkokin kiwon lafiya a ciki da wajen Nijeriya.

 

Tare da  Al-Amin Ciroma

 (08033225331)
ciroma14@yahoo.com Tare da  Al-Amin Ciroma

 (08033225331)

Exit mobile version